Da Dumi-Dumi: Atiku ya gana da Gwamna Wike bayan lallasa shi a zaɓen fidda gwanin PDP

Da Dumi-Dumi: Atiku ya gana da Gwamna Wike bayan lallasa shi a zaɓen fidda gwanin PDP

  • Atiku Abubakar, ɗan takarar da jam'iyyar PDP ta tsayar a zaɓen shugaban kasa ya gana da gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas a Abuja
  • Tsohon mataimakin shugaban ya yi haka ne a wani yunkuri na sulhu da gwamnan, wanda shi ne ya zo na biyu a samun kuri'u
  • Kafin fara kaɗa kuri'a a zaɓen fidda gwanin PDP, Wike ya ce zai goyi bayan duk wanda ya samu nasara

Abuja - Ɗan takarar da jam'iyyar PDP ta tsayar a zaɓen shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya gana da gwamnan Ribas, Nyesom Wike a Abuja, kamar yadda Punch ta tattaro.

Tsohon shugaban ƙasan ya lallasa Gwamna Wike a zaɓen fid da gwani na jam'iyyar PDP wanda ya gudana a birnin Abuja ranar Asabar.

Bayanai sun nuna cewa taron na ranar Litinin ya gudana ne da nufin sulhunta jiga-jigan siyasar guda biyu a wani yunkuri na fafata wa da APC a babban zaɓen 2023 dake tafe.

Kara karanta wannan

Bayan shan kaye hannun Atiku, Gwamnan arewa ya fara shirin kwace tikitin takarar gwamna a jiharsa

Atiku Abubakar ya gana da Wike a Abuja.
Da Dumi-Dumi: Atiku ya gana da Gwamna Wike bayan lallasa shi azaɓen fidda gwanin PDP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Taron ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Ekiti kuma ɗaya ɗaga cikin yan takarar da suka sha kaye, Ayodele Fayose, da sauran jiga-jigan PDP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin zaɓen wanda ya gudana a Filin Moshood Abiola Stadium, Atiku ya samu kuri'u 371, wanda ya ba shi damar lallasa abokan takara musamman Wike da ya sami kuri'u 237 da sauran su.

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Deleget sun sha mamaki yayin da gwamnan Sokoto kuma dan takarar shugaban ƙasa, Aminu Tambuwal, ya janye kuma ya umarci masoyansa su zaɓi Atiku.

Wata majiya ta kara da cewa gwamnan ya yi haka ne sanadin shigar ƙungiyar dattawan arewa cikin lamarin, waɗan da ke fafutukar ganin yan takarar arewa sun sulhunta kan su.

Zan koma bayan duk wanda ya ci nasara - Wike

Da yake jawabi kafin fara kaɗa kuri'a a wurin zaben fid da gwanin, Gwamna Wike ya ce zai goyi bayan duk wanda ya samu nasarar lashe zaɓen.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Mako ɗaya bayan Murabus, Ministan Buhari ya lashe tikitin gwamna a APC

Amma sai aka neme shi aka rasa a saman munbari lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ke jawabin godiya bayan cin nasara.

Har yanzun gwamna Wike bai ce uffan ba tun bayan shan kaye a zaben na ranar 28 ga watan Mayu, 2022.

A wani labarin na daban kuma Jam'iyyar APC ta fara tantance yan takarar shugaban ƙasa da ke son gaje Buhari

Jam'iyyar All Progressive Congress wato APC ta fara aikin tantance yan takarar shugaban ƙasa waɗan da ke yunkurin gaje shugaba Buhari a zaɓen 2023.

Tantancewar ta fara gudana ne a sirrance a wani shahararren Hotel da ke babban birnin tarayya Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262