NNPP ta shiga gidan tsohon Ministan Buhari, ‘Dan Majalisan Kano ya fice daga APC

NNPP ta shiga gidan tsohon Ministan Buhari, ‘Dan Majalisan Kano ya fice daga APC

  • Hon. Shamsudeen Bello Dambazau ya yi watsi da APC zuwa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari
  • ‘Dan majalisar yace ta shi ba ta zo daya da APC ba, don haka ya tsallaka zuwa jam’iyyar adawar
  • Dambazau ya yi ta faman shari’a da Siraju Idris da Kawu Sumaila kafin ya dare kujerarsa a 2019

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - A karshen makon jiya mu ka ji Shamsudeen Bello Dambazau ya sauya-sheka daga jam’iyyar APC mai mulki, zuwa NNPP mai hamayya.

Hon. Shamsudeen Bello Dambazau ya bada sanarwar ficewarsa daga APC a shafinsa na Twitter da yammacin Ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu 2022.

‘Dan majalisar tarayyan ya tabbatar da cewa ya sauya-sheka ne, a dalilin girmamawar da yake yi wa jagoran Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Kamar yadda Shamsudeen Bello Dambazau ya bayyana a shafin na sa a jiya, ya dauki wannan mataki ne bayan ya tattauna da mutane da mabiyansa.

Kara karanta wannan

Jonathan ba ‘Dan Jam’iyyarmu ba ne, ba za mu ba shi takara ba inji Mataimakin Shugaban APC

Dambazau shi ne ‘dan majalisa mai wakiltar yankin Takai/Sumaila a majalisar wakilan tarayya.

Shamsudeen Bello Dambazau
Shamsudeen Bello Dambazau tare da Gwamnan Kano Hoto: HonDambazauMHR
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina mai alfahari da samun damar taimakawa wajen gina kasa a karkashin jam’iyyar APC.”
“Sai dai abubuwan da suke faruwa a cikin jam’iyyar, sun sa ba zai yiwu in cigaba da taka rawar gani ta hanyar da za ta taimakawa jam’iyyar ba.”
“Azamata ta ceto mutanen mazabata da kuma jihar Kano tana nan duk da cewa na canza gida a siyasa.”
“Ina mai mika godiya na damar da aka bani domin hidimtawa a karkashin jam’iyyar, amma lokaci ya yi da zan komawa tsagin da ta mu ta zo daya.”

Legit.ng ta fahimci Shamsudeen Dambazau yana cikin wadanda suka gagara samun takarar tazarce a APC, bai lashe zaben fitar da gwani da aka gudanar ba.

Mahaifinsa, Abdulrahman Dambazzau ya rike shugaban hafsun sojojin kasa, sannan ya yi Ministan harkokin gida a wa’adin farko na Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Jerin abubuwa 10 da suka jawo Atiku Abubakar ya dankara Wike da kasa a zaben PDP

'Yan Majalisan Jigawa sun sha kashi

Ku na da labari a cikin duka Sanatocin Jigawa, babu wanda zai koma kan kujerarsa a karkashin jam’iyyar APC. Haka lamarin ya ke ga 'yan majalisar wakilai hudu.

Rade-radi na yawo cewa akwai 'yan majalisar dokoki fiye da 11 da ba za su yi takara a APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng