2023: Gudaji Kazaure Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin APC a Jigawa, Akwai Yiwuwar Zai Koma NNPP

2023: Gudaji Kazaure Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin APC a Jigawa, Akwai Yiwuwar Zai Koma NNPP

  • Fitaccen dan majalisar wakilai, Muhammad Kazaure, a ranar Asabar ya fadi zaben fidda gwani, yanzu ba shi ba ne wanda APC za ta tsayar
  • Dama shi ne dan majalisa mai wakiltar mazabar Kazaure/Roni/Gwiwa da Yankwashi a Jihar Jigawa kuma ya yita rikici da gwamnan jihar
  • Mukhtar Zanna ne ya kayar da shi yayin da ya samu kuri’u 89, Muhammad Zakari ya samu kuri’u 70 sai Kazaure ya bige da kuri’u 26

Jigawa - Muhammad Kazaure, fitaccen dan majalisar nan mai wakiltar mazabar Kazaure/Roni/Gwiwa da Yankwashi a Jihar Jigawa na majalisar tarayya bai samu tikitin tsayawa takara ba a jam’iyyar APC, Premium Times ta ruwaito.

Kazaure ya na da jikakkiya da Gwamna Muhammad Badaru na jihar, tare da kuma jam’iyyar, reshen jihar Mukhtar Zanna, shugaban karamar hukumar Kazaure ne ya kayar da shi.

Kara karanta wannan

Shugaban kungiyar Malamai ya doke Sanata wajen zama ‘Dan takarar Gwamna a APC

2023: Gudaji Kazaure ya sha kaye a zaben fidda gwanin APC a Jigawa
2023: Mohammed Kazaure ya sha kaye a zaben fidda gwanin APC a Jigawa. Hoto: Premium Times.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zanna ya samu kuri’u 89, na kusa da shi kuma Muhammad Zakari mai kuri’u 70 yayin da Kazaure ya samu kuri’u 26.

Muhammad Alhassan, wanda soja ne mai murabus, sannan ya rike mukamin Kwamishinan Noma a jihar, ya samu kuri’u 8, sai Abdullahi Mainasara mai kuri’u 7.

Magaji Da’u-Aliyu yanzu haka dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Birnin Kudu da Buji a majalisa tarayya.

Da’u-Aliyu ma yana da jikakkiya da gwamnan jihar amma duk da haka, ya samu kuri’u 87, inda ya zarce wa abokin takararsa, Nasidi wanda ya samu kuri’u 13.

Ba a sanar da sakamakon zaben fidda gwanin mazabar Hadejia, Auyo da Kafin-Hausa ba tukunna.

Premium Times ta bayyana jerin sunayen ‘yan takarar da su ka lashe zaben fidda gwanin kamar haka:

1. Hon Makki Abubakar Elleman - Na mazabar Malam Madori da Kaugama.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwani: An sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a Sokoto

2. Injiniya Magaji Da’u Aliyu - Na mazabar Buji da Birnin Kudu.

3. Hon. Ibrahim Abdullahi Kemba - Wanda ya lashe zaben mazabar Dutse da Kiyawa.

4. Hon. Yusuf Sa’idu Miga - Mazabar Jahun da Miga.

4. Hon. Abubakar Hassan Fulata - Mazabar Birniwa, Guri da Kiri-Kasamma.

Ana

Akwai yiwuwar Kazaure ya koma NNPP

Shafin Jam'iyyar NNPP a Twitter ya wallafa hoton Kazaure tare da rubutu da ke nuna cewa ya bar APC ya koma jam'iyyar mai kayan marmarin.

Sai dai a halin yanzu ba a ji daga bakinsa shi Gudaji Kazauren ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164