Tinubu: Zan Tabbatar An Dena Ɗauke Wutar Lantarki a Najeriya Idan Aka Zaɓe Ni Shugaban Ƙasa a 2023
- Jagoran jam'iyyar APC na kasa kuma mai neman takarar shugaban kasa ya yi alkawarin samar da lantarki babu dauke wa cikin shekaru hudu idan an zabe shi
- Tinubu, cikin wata sanarwa da hadiminsa Bayo Onanuga ya fitar ya ce gwamnatinsa za yi aiki don samar da lantarki mega wata 15,000 da za a rika rabarwa a kasar
- Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya kuma ce zai kirkiri sabbin hukumomi shida a kowanne shiyar kasar da zai mayar da hankali wurin amfani da albarkatun da ke shiyoyin don habbaka su
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Bola Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas kuma mai neman tikitin takarar shugaban kasa a APC ya ce idan aka zabe shi shugaban kasa, cikin shekaru hudu, zai yi aiki tukuru don ganin an dena dauke lantarki, The Cable ta rahoto.
Rashin ingantaccen wutar lantarki a Najeriya ya dade yana ci wa kasar tuwo a kwarya, inda lantarkin kasar ya samu matsala a kalla sau 200 cikin shekaru 10 da suka gabata.
Megawatt 15,000 na lantarki za a rika rabarwa yan Najeriya - Tinubu
Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a ta bakin hadiminsa Baya Onanuga, tsohon gwamnan na Legas ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar tana rabar da megawatta na lantarki 15,000 a sassan kasar, Information Ng ta rahoto
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"A bangaren lantarki, zan mayar da hankali don daukan matakin gaggawa nan take don warware kallubalen tashohin samar da lantarki, siyan iskar gas, farashi da rarraba lantarki," kamar yadda aji jiyo yana cewa.
"Abin da gwamnati za ta saka a gaba shine samar da megawatt 15,000 na lantarki da za a rarraba wa masu amfani da lantarki a sassar kasar don tabbatar da samun lantarki da dauke wa cikin shekaru hudu masu zuwa."
Zan kafa sabbin hukumomin gwamnati na musamman a shiyoyin Najeriya shida - Tinubu
Baya ga lantarkin, Tinubu ya yi alkawarin gina tattalin arzikin kasar ta hanyar habbaka GDP cikin shekaru hudun tare da farfado da masana'antu.
Tsohon gwamnan na Legas ya kuma ce idan aka zabe shi shugaban kasa, zai kirkiri sabbin hukumomi shida a kowanne shiyar kasar da zai mayar da hankali wurin amfani da albarkatun da ke shiyoyin don habbaka su.
Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya
A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.
Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.
2023: Atiku Ya Bayyana Manufofi 5 Da Zai Yi Amfani Da Su Don Tsallakar Da Najeriya Zuwa Ga Tudun Mun Tsira
Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.
Asali: Legit.ng