Yanzu-Yanzu: INEC ta tsawaita wa'adin zaben fidda gwanin jam'iyyu da kwanaki 6
- Hukuamar zabe mai zaman kanta ta sanar da karin wa'adi ga jam'iyyun siyasa domin su tattara sakamakon zaben fidda gwani
- Wannan na zuwa ne bayan kiraye-kiraye daga jam'iyyun kan karancin lokacin da suke fuskanta a zaben da ke gudana
- A halin da ake ciki, INEC ta ce bata sauya jadawalin tafiyar da ayyukan zabe ba, kawai dan karin wa'adi ne don tattara bayanai
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta yi karin wa'adin zaben fidda gwani ba tare da sake duba ga jadawalin hidimomin jam'iyyun siyasa ba kafin babban zaben 2023 mai zuwa, inda ta tsawaita wa'adin da kwanaki shida.
Wannan na zuwa ne bayan da jam'iyyun siyasar kasar nan suka nuna bukatar tsawaita lokacin domin samun gudanar da ayyukansu cikin tsanaki kamar dai yadda hukumar ta INEC ta bayyana a cikin sanarwar da ta fitar.
Sai dai, bayanan da INEC ta yi sun nuna cewa, ba wai sauya komai daga jadawalin ayyukan zaben ta yi ba, kawai hukumar ta ba jam'iyyun siyasa damar tattara bayanan da suka shafi 'yan takarar da suka yi nasara a zabukan fidda gwanin ne.
Wata sanarwar da wakilin Legit Hausa ya samo daga hukumar INEC ta bayyana cewa, karin ba zai shafi jadawalin ba, saboda babu abin da INEC za ta yi a cikin kwanakin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Hukumar ba ta shirya yin komai a wannan lokacin ba. Manufar ita ce kawai a ba wa jam’iyyu lokaci don tattara jerin sunayen ‘yan takarar da suka zaba kafin a tura bayanan zuwa sahar ‘yan takara ta INEC daga 10th - 17th June 2022."
Zaben fidda gwani: An sanar da wanda ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a Sokoto
A wani labarin, tsohon mataimakin gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya zama wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC a jihar Sokoto, TVC ta ruwaito.
Aliyu, ya samu kuri’u 1,080 daga cikin jimillar kuri’u 1,182 da aka kada a zaben fidda gwani da ‘yan takara shida suka fafata a ciki.
Shugaban kwamitin zaben, Aliyu Kyari, ya ce Ibrahim Gobir ya samu kuri’u 36, Faruk Malami-Yabo ya samu kuri’u 27, sai kuma tsohon ministan sufuri, Yusuf Suleiman ya samu kuri’u 16 da kuri’u 23 da kuma kuri'un da suka lalace.
Asali: Legit.ng