Yadda 'yan siyasa suka ingiza ni yin takara, suka dinga karbe min sulalla, Tsohon IG

Yadda 'yan siyasa suka ingiza ni yin takara, suka dinga karbe min sulalla, Tsohon IG

  • Wani tsohon sifeta-janar na 'yan sandan Najeriya, Mike Okiro ya bayyana yadda wasu 'yan siyasa suka mayar da shi talaka fitik a lokacin da ya nemi kujerar Sanata bayan ya yi ritaya
  • Shugaban 'yan sandan ya koka ne a kan halayyar mutane na bukatar kudi daga hannun 'yan takara ba tare da dubi da sun cancanta ko akasin haka ba
  • Ya ja kunnen 'yan Najeriya da su guji saida kuri'unsu sannan su zabi wanda suke ganin ya cancanta ba tare da dubi da inda ya fito ko jam'iyya ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani tsohon sifeta-janar na 'yan sanda (IGP), Mike Okiro ya bayyana yadda wasu 'yan siyasan da bai ambaci sunansu ba suka maida shi talaka fitik a lokacin da ya nemi takarar sanata bayan ya yi ritaya.

Okiro, wanda ya yi jawabi a Abuja a wani shiri mai taken: "Kafar tattaunawar 'yan takarar shugaban kasa" wanda New Nigeria Dream intiative (NNDI) ta shirya, ya bayyana yadda wasu tawagar mutane suka shirya masa tuggun shiga siyasa bayan ya yi ritaya inda daga bisani suka amshe masa kudade har ta kai ga ba shi da ko asi.

Kara karanta wannan

Babu banbancin tsakanin Deleget da dan bindiga mai karbar kudin fansa, Shehu Sani

Yadda 'yan siyasa suka ingiza ni yin takara, suka dinga karbe min sulalla, Tsohon IG
Yadda 'yan siyasa suka ingiza ni yin takara, suka dinga karbe min sulalla, Tsohon IG. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dattijon ya zargi 'yan Najeriya da yawan amsar kudi daga 'yan siyasa a lokacin da suke neman a zabe su, inda ya ce su ne matsalolin gwamnati kuma "mun fi 'yan siyasa laifi."

Daily Trust ta ruwaito cewa, tsohon shugaban 'yan sandan sannan sifeta-janar na 13 wanda ya yi aiki tsakanin shekarar 2007 zuwa 2009 ya ja kunnen 'yan Najeriya da su ce "ya isa haka" a 2023 ta hanyar kin amincewa da kudaden 'yan siyasa yayin zabe.

A cewarsa, "'Yan Najeriya za su yi magana a kan rashin shugabanni na kwarai, amma ina cewa a'a, ba wannan bane kadai! Matsalar daga bangarori biyu ne! Idan shugabanni na da aibi, muna da mabiya marasa hangen nesa! Saboda idan shugabanni suna yin abubuwa, dariya kawai muke yi, muna daga musu hannu tare da cewa taka lafiya! Hakan ke sa su sake maimaita irin abun da suka yi a baya.

Kara karanta wannan

Soja ya bindige abokin aikinsa yayin arangama da 'yan kungiyar asiri a Ogun

"Amma idan muka ce ba zai yuwu ba! Ya isa haka, sai su gyara! Ka je sun baka kudi ka zabe su ba tare da la'akari da wannan mutumin zai iya aiki yadda ya dace ko akasin haka ba! Sun baku N5,000 ka sha wahala na shekaru hudu. Hakan na nufin wannan N5,000 din ita ce kudin sallamar ka na shekaru hudu.
"Na yi takarar kujerar sanata a nan Abuja. Ina zaman zamana suka kira ni in fito takara. Na ce ban dade da ritaya ba, suka ce a'a ka zo ka yi takara! Na ce shikenan, zan yi shawara da mata ta. Na shaida wa mata ta tace ina jin tsoro.
"Sai su zo wuri na su ce min muna so mu je wuri kaza, kawo kudi; muna son yin kaza, kawo kudi; muna so mu yi wannan, kawo kudi; sai da na basu duk abun da na tara, har ta kai ga bani da abun badawa. Wata rana suka zo, na ce bazan bada ko sisi ba saboda bani da abun baku.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja

"Suka ce min wancan mutumin baya yin abun da ya dace amma in zo in gwada. Kuna so in cigaba da baku amma a ina zan samu kudi? Na ce shikenan, bari mu yi wannan, misali yanzu naje na ari kudi ko na siyar da kadara ta don in ba ku kudi, kuma aka zabe ni, tabbas, abun da zan fara yi shi ne in biya bashin da ake bi na da dukkan kadarorin da na siyar in ga na sake mallakarsu.
"Na san bayan shekaru hudu, za a sake wani zaben, zan adana kudi don wannan zaben yadda ba zan sake ranto kudi ba. Ku mutane ku ne matsalar gwamnati. Mu daina amincewa da masu siyan kuri'u."
Ya kara da cewa, "Ba za mu bi miyagun iri ba, za mu zabi mutane ba tare da dubi da jam'iyyunsu ba. Za mu bi cancanta.
"Ku duba nagartar mutum! Ku duba idan ya cancanta, ba daga inda suka fito ba, kuma ba tare da dubi da jam'iyya ba, don tabbatar da idan suka mulke mu, romon damakaradiyya zai riski kowa."

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng