Soja ya bindige abokin aikinsa yayin arangama da 'yan kungiyar asiri a Ogun

Soja ya bindige abokin aikinsa yayin arangama da 'yan kungiyar asiri a Ogun

  • Gari ya cakude kuma al'amura sun jagule yayin da wani jami'in soja ya bindige abokin aikinsa bayan arangama da wasu da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne
  • Lamarin ya auku ne bayan rikici ya barke tsakanin kungiyoyi 2 na 'yan damfarar yanar gizo, yayin da daya daga cikin kungiyar ta gayyaci 'yan sara suka su farwa daya, ita kuma daya ta gayyaci sojoji su shiga lamarin
  • Yayin da hatsabiban suka yi ido biyu da jami'an sojin, nan take suka fara jifansu da duwatsu da kwalabe, hakan yasa sojan a kokarin saita bindigarsa amma sai aka yi rashin sa'a ya harbi abokin aikinsa

Ogun - Rikici ya barke a ranar Laraba a yankin Ibafo na jihar Ogun yayin da wani soja ya bindige abokin aikinsa a lokacin da ya yi arangama da wasu da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne.

Kara karanta wannan

Abba Kyari ya sha da kyar, saura kiris masu fushi da shi su hallaka shi a gidan yari

Daily Trust ta tattaro yadda wasu daga cikin kungiyoyin 'yan damfarar yanar gizo da aka fi sani da Yahoo Boys suka kai wa juna hari a kan wani lamari da ya hada su.

Soja ya bindige abokin aikinsa yayin arangama da 'yan kungiyar asiri a Ogun
Soja ya bindige abokin aikinsa yayin arangama da 'yan kungiyar asiri a Ogun. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daya daga cikin kungiyoyin ya dauki hayar 'yan sara suka don su kai farmaki ga dayan kungiyar, wadanda daga bisani suka gayyaci sojoji.

Ganau ya bayyana yadda 'yan kungiyar asiri suka yi ido biyu da jami'an sojoji a yankin cikin wata motar gida, "A nan take suka fara jifansu da duwatsu, kwalabe da sauransu."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro yadda fusataccen jami'in sojin ya yi kokarin saita bindigarsa; amma sai ya yi kuskuren harbin abokin aikinsa.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"Wasu 'yan damfarar yanar gizo da ke da matsala da junansu. Wata kungiya ta gayyaci 'yan kungiyar asiri, yayin da wasu suka gayyaci sojoji.

Kara karanta wannan

Kashe-kashe a Kudu maso Gabas: Ku tsammanci martani mai tsauri daga gareni, Buhari ga 'yan IPOB

"Sojojin sun je gurin da lamarin ya auku a motar gida. Sun kai samame ga wasu hatsabibai da ake tunanin 'yan kungiyar asiri ne. Mun gano yadda daya daga cikin sojojin ya yi kuskuren budewa abokin aikinsa wuta, wanda a halin yanzu aka garzaya da shi asibiti.
"Jami'anmu na kan lamarin, kuma an samu daidaito a wurin," a cewar Oyeyemi.

Tashin hankali: Sojoji sun kashe sufeto na 'yan sanda da duka a Najeriya

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Ribas ta bayyana sufeton ta da take zargin sojoji sun kashe da duka a jihar.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, ya bayyana jami'in dan sandan da suna Hosea Yakubu, inda ya kara da cewa har yanzu suna cigaba da bincike akan lamarin.

An gano cewa wasu sojoji dake gadin wani kamfani ne suka kashe wannan dan sanda bayan ya karya dokar bin hanya a gaban kamfanin a ranar Lahadi 16 ga watan Agusta, 2020.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna, cikin har da dan kasar Pakistan

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: