Yanzu-Yanzu: Kotu ta Halasta Wa Jonathan Yin Takarar Shugaban Kasa a 2023

Yanzu-Yanzu: Kotu ta Halasta Wa Jonathan Yin Takarar Shugaban Kasa a 2023

  • Ana kwana guda zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa na APC, kotu ta ce Goodluck Jonathan zai iya yin takara a 2023
  • A kwanakin baya, an rika tafka muhawara kan cancantarsa duba da cewa akwai doka da ta ce idan mataimaki ya karasa wa'adin mai gidansa tamkar ya yi nasa ne
  • Sai dai a hukuncinta, kotun ta ce an kafa wannan dokar ne bayan Jonathan ya yi wa'adin Yar'adua don haka dokar ba za ta yi aiki a kansa ba don lokacin da ya yi mulkin ba a yi dokar ba

Bayelsa - Babban kotun tarayya da ke Yenagoa, Jihar Bayelsa, ta yanke hukunci cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan zai iya yin takarar shugabancin kasa a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Dumi: Sanatan PDP ya fice daga jam'iyyar, ya koma APGA zai nemi takara a 2023

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jam'iyyar ta yanke hukuncin ne ranar jajiberin zaben fidda gwani na yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ta APC.

An alakanta Jonathan da jam'iyyar APC mai mulki a yanzu bayan siya masa fom din takarar shugaban kasa kan Naira miliyan 100.

Yanzu-Yanzu: Kotu Halasta Wa Jonathan Yin Takarar Shugaban Kasa a 2023
Kotu Halasta Wa Jonathan Yin Takarar Shugaban Kasa a 2023. Hoto: Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma, an riga bayyana mabanbanta ra'ayoyi kan cancantarsa shiga takarar shugabancin kasar.

Sai dai, a ranar Juma'a, kotun ta ce Jonathan, wanda ya sha kaye a zaben 2015 a hannun Shugaba Muhammadu Buhari, yana iya neman kujerar shugaban kasar, The Punch ta rahoto.

Sai bayan da Jonathan ya karasa wa'adin Yar'Adua aka yi dokar, don haka ba za ta yi aiki a kansa ba - Kotu

Alkalin, Mai shari'a Isa Hamma Dashen, wanda ya bada hukuncin a ranar Juma'a, ya ce dokar da aka kafa daga baya ba za ta shafi takarar Jonathan a 2023 ba.

Kara karanta wannan

Karin bayani: APC ta sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna a bauchi

A karar da Andy Solomon da Idibiye Abraham suka shigar, sun nemi kotun ta tabbatar da cewa dokar da aka yi daga baya na hana mataimakan shugaba da suka gaji shugabanninsu yin mulki sau biyu bata shafi Jonathan ba.

Jonathan ya karbi mulki a hannun marigayi Yar'adua ne bayan ya rasu a 2010 kuma ya sake takara a 2011 ya ci zabe.

Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.

Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164