Da dumi-dumi: Umar Bago ya lashe zaben fidda dan takarar gwamnan APC a Neja
- A karshe jam'iyyar All Progressives Congress(APC) ta fitar da dan takararta na gwamna a jihar Neja wanda shine zai daga tutarta a babban zabe mai zuwa
- Umar Mohammed Bago ne ya yi nasarar mallakar tikitin jam'iyyar a zaben fidda gwanin da aka gudanar
- Bago ya samu kuri’u 540 wajen kayar da manyan yan takara tara ciki harda mataimakin gwamna mai ci, Alhaji Ahmed Ketso
Niger - Umar Mohammed Bago ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na takarar kujerar gwamnan jihar Neja a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress(APC), jaridar The Nation ta rahoto.
Bago wanda ya kasance dan majalisa mai wakiltan mazabar Chanchaga a majalisar wakilai ta tarayya ya kayar da yan takara tara a zaben.
Da yake sanar da sakamakon zaben, Alhaji Nasiru Ibrahim, shugaban kwamitin zaben fidda gwani na takarar gwamnan Neja, ya bayyana cewa gaba daya adadin kuri’un da aka kada 1,049 inda kuri’u 11 suka lalace.
Umar Bago ya samu kuri’u 540 wajen mallakar tikitin na APC, inda babban abokin hamayyarsa Idris Malagi ya samu kuri’u 386 yayin da Sani Ndanusa ya samu kuri’u 84.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa Alhaji Ahmed Ketso ya samu kuri’u 17 yayin da Mista Mohammed Rufai-Mohammed ya samu kuri’u hudu sannan Mista Idris Usman ya samu kuri’u uku.
Hakazalika ya bayyana cewa Mohammed Nda, Aliyu Idris da Mohammed Kputagi sun samu daddaya kowannensu.
Ya ce sauran yan takarar basu samu ko daya ba, jaridar PM News ta rahoto.
Aisha Binani ta lallasa mazaje biyar, ta lashe zaben fidda gwanin APC a Yola
Zaben fidda gwanin PDP: Jerin gwamnoni da mataimakan gwamnoni da suka lashe tikitin majalisar dattawa
A wani labarin, Sanata Aishatu Binani ta lallasa gardawa biyar a zaben fidda gwanin yan takaran gwamnan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Adamawa.
Binani ta zama mace ta farko da ta lashe zaben fidda gwanin APC a jihar Adamawa.
Aishatu Binani wacce yanzu haka Sanata ce mai wakiltar Adamawa ta tsakiya ta lallasa tsohon gwamnan jihar, Jibrilla Bindow da tsohon Shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu.
Asali: Legit.ng