Da Dumi-Ɗumi: Tsohon gwamnan Zamfara ya janye karar da ya maka APC da Matawalle

Da Dumi-Ɗumi: Tsohon gwamnan Zamfara ya janye karar da ya maka APC da Matawalle

  • Bayan yin maslaha, tsohon gwamna Abdul-aziz Yari ya umarci a janye duk ƙarar da ya shigar da jam'iyyar APC a Kotu
  • Tun bayan sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle zuwa APC, rikici ya ɓarke kan tsagin da zai jagoranci jam'iyya
  • Sanata Kabiru Marafa ya ce a halin yanzun mambobin APC a Zamfara sun koma inuwa ɗaya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Alhaji Abdulaziz Yari, ya ba da umarnin gaggawa na janye kara uku da ya shigar da shugabancin jam'iyyar APC.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na zuwa ne bayan sulhun da aka yi tsaganin ɓangarorin APC biyu na Zamfara.

Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya sasanta tsagin Gwamna Bello Matawalle da tsagin tsohon gwamna Yari da Sanata Kabiru Marafa.

Kara karanta wannan

Hotuna: Zulum ya ci zaben fidda gwani, ya ki fitowa takarar VP, ya ce sake gina Borno ne a gabansa

Tsohon gwamnan Zamfara, Abdul-Azizi Yari.
Da Dumi-Ɗumi: Tsohon gwamnan Zamfara ya janye karar da ya maka APC da Matawalle Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wannan sulhu da aka samu tsakanin ɓangarorin ya bude sabon shafi na harkokin siyasar jam'iyyar APC mai mulki reshen jihar Zamfara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kafin samun masalaha a tsakanin, saɓanin jiga-jigan siyasa a Zamfara ya haddasa darewar jam'iyyar APC har aka samu shugabanni biyu.

Duk wani yunkuri na kawo karshen sabanin ɗake tsakani da kwamitin rikon kwarya karkashin gwamna Mai Mala Buni, ya yi a wancan lokacin bai haifar da ɗa mai ido ba.

APC ta dunƙule wuri ɗaya a Zamfara

Wata majiya ta ce sanarwan janye karar ta fito ne daga hannun Sanata Marafa jim kaɗan bayan kammala taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana a Garba Nadama Hall, Gusau, ranar Laraba.

Marafa ya faɗa wa dandazon mutane cewa zasu janye karan ne domin tabbatar da sulhun da kuma baiwa gwamna Matawalle goyon bayan da ya dace wajen shawo kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani gwamna ya lashe zaben fidda gwanin APC, zai nemi tazarce a 2023

Ya ce: "Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta dunƙule wuri ɗaya karkashin shugabanci ɗaya kuma dukkan ƴaƴan jam'iyya na aiki tare cikin zaman lafiya da cigaban jiha."

A wani labarin kuma Yan majalisar wakilai ta tarayya guda 6 sun yi amai sun lashe, sun koma PDP daga APC

Yayin da jam'iyyar APC ke ganin ta shawo kan rikicin da ya addabeta a Zamfara, wata sabuwar ɓaraka ta sake barkewa.

Yan majalisar wakilan tarayya guda 6 da suka bi gwamna zuwa APC sun lashe aman su, sun sake komawa jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262