Yan majalisar wakilai ta tarayya guda 6 sun yi amai sun lashe, sun koma PDP daga APC

Yan majalisar wakilai ta tarayya guda 6 sun yi amai sun lashe, sun koma PDP daga APC

  • Yayin da jam'iyyar APC ke ganin ta shawo kan rikicin da ya addabeta a Zamfara, wata sabuwar ɓaraka ta sake barkewa
  • Yan majalisar wakilan tarayya guda 6 da suka bi gwamna zuwa APC sun lashe aman su, sun sake komawa jam'iyyar PDP
  • Hakan ta faru ne biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma wa ta sulhu tsakanin Matawalle, Abdul-Aziz Yari da kuma Sanata Marafa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Zamfara - Mambobin majalisar wakilan tarayya daga jihar Zamfara guda Shida waɗan da suka koma jam'iyyar APC tare da gwamna Matawalle sun yi amai sun lashe.

Leadership ta rahoto cewa yan majalisar wakilan sun sake komawa jam'iyyar PDP kuma sun karɓi tikitin takara a babban zaɓen 2023 ba tare da hamayya ba.

Jam'iyyar APC da mai hamayya PDP.
Yan majalisar wakilai ta tarayya guda 6 sun yi amai sun lashe, sun koma PDP daga APC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Mambobin majalisar sun sake komawa PDP ne sakamakon yarjejeniyar da aka yi yayin sulhun gwamna Bello Matawalle na Zamfara, tsohon gwamna Abdul-Aziz Yari da Sanata Kabiru Marafa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar APC ta hana yan majalisun damar siyan Fom ɗin tsayawa takara a zaɓen 2023 saboda ta riga da ta bai wa wasu sabbi kujerun su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jerin sunayen yan majalisun da suka koma PDP

Tofaffin mambobin APC da suka yi amai suka lashe suka koma PDP sun haɗa da, Honorabul Ahmad Maipalace na mazaɓar Gusau/Tsafe, Honorabul Bello Hasan na mazaɓar Shinkafi/Zurmi da Honorabul Sulaiman Gummi na mazaɓar Gummi/Bukkuyum.

Sauran su ne; Honorabul Sani Umar na mazaɓar Kaura-Namoda/Birnin Magaji, Honorabul Shehu Ahmad na mazaɓar Mary/Bungudu, da kuma Honorabul Ahmad Muhammed mai wakiltar mazaɓar Bakura/Maradun a majalisar tarayya.

A wani labarin na daban kuma Sanata da wasu yan takara 6 sun janye daga zaben fidda gwanin PDP, jerin sunayen su

Yan takarar guda 7 sun sanar da matakin janyewar ne bayan wani taron gaggawa da suka yi a gida n tsohon sakataren gwamnatin Abia.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Kwankwaso da wasu yan majalisu sun fice daga NNPP, sun koma APC

A halin yanzun sun bar mutum biyu kacal su fafata a zaɓen f itar da ɗan takara ɗaya tilo da zai kare martabar PDP a babban zaɓen gwamna 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel