Yanzu-Yanzu: Goodluck Jonathan ya yi raddi kan zaɓen fidda gwanin PDP da APC

Yanzu-Yanzu: Goodluck Jonathan ya yi raddi kan zaɓen fidda gwanin PDP da APC

  • Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, ya nuna takaicinsa kan yadda yan takara ke sayen Deleget don su zaɓe su
  • Jonathan ya kira zaɓukan tsayar da yan takara da ke gudana a sassan ƙasar nan da 'Datti' domin duk an sauka kan tsarin da ya kamata
  • Tsohon shugaban ya bukaci majalisa ta yi dokar da zata haramta raba wa Deleget kuɗi kuma ta share sashi na 84

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, ya yi Alla-wadai da zaɓen fid da gwani da ke gudana yanzu haka na babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Daily Trust ta ruwaito cewa an samu wasu bayanai da suka nuna yadda yan takara ke jawo hankalin Deleget da kuɗi domin su zaɓe su.

Legit.ng ta kawo muku rahoton yadda ɗan tsohon mataimakin Jonathan, Namadi Sambo, ya buƙaci Deleget ɗin da suka karɓan masa kudi kuma ba su zaɓe shi ba su dawo masa da kuɗaɗensa.

Kara karanta wannan

Yadda Sanata Okorocha ya kwanta a kasa yana rokon a taimaka masa yayin da EFCC ta kutsa kai gidansa

Tsohon shugaban ƙasa Jonathan.
Yanzu-Yanzu: Goodluck Jonathan ya yi raddi kan zaɓen fidda gwanin PDP da APC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Alhamis, Jonathan ya yi jawabi a wurin kaddamar da littafi mai suna, "Gwamnatin jam'iyyar siyasa" wanda Dr. Muhammed Wakil, tsohon ƙaramin ministan wuta ya rubuta.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A jawabinsa Jonathan ya ce abun kunya ne ka biya Deleget kudi don su zaɓe ka kuma ka dawo kana neman su dawo maka da kudinka bayan ka gaza samun tikitin takara.

Jonathan ya ce:

"Baki ɗaya waɗan nan zabukan fitar da yan takaran da ke cigaba da gudana a faɗin ƙasar nan datti ne kawai. Wannan ba shi ne ainihin yadda ake yi ba, matakan da ake bi ba dai-dai bane."
"Baki ɗaya zabukan ba haka ake yin su ba kuma ba zai haifar wa ƙasar nan ɗa mai ido ba. Amma hakanan zamu yi hakuri a tafi a haka."
"Muna Addu'a Allah ya kawo mana mutane nagari. Ba na fatan abubuwan da suka faru a ƙasar nan a wannan shekarar 2022 ya sake faruwa nan gaba."

Kara karanta wannan

2023: Wani ɗan takara a PDP ya yanke jiki ya faɗi bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani

Jonathan ya roki majisar tarayya

Tsohon shugaban ƙasan ya roki majisun tarayya su yi doka wacce zata maida sayen Deleget da sauran masu kaɗa kuri'a ya zama babban laifi.

"Ba zai yuwu majalisa ta yi dokoki ta garƙame jam'iyyu wuri ɗaya ba, kowace jam'iyya na da hanyar tsaida ɗan takara kuma suna da matakan su a kundin mulkin su."
"Kirkirar wani yanayi da zai sa jam'iyyu su zaɓi yan takara ta hanya ɗaya rashin hankali ne, jam'iyyun siyasa ba wasu ɓangaren gwamnati bane."
"Bai kamata majisa ta yi dokar da zata maƙare jam'iyyu wuri ɗaya ba, ya kamata a goge sashi na 84 daga kundin dokokin zaɓe."

A wani labarin kuma Bidiyon yadda Kakakin majalisa ya duƙa kan guiwa yana gode wa gwamna bayan lashe zaɓen fidda gwanin PDP

An hangi kakakin majalisar dokokin jihar Delta a wani bidiyo ya duka kan guiwarsa yana mai godiya ga gwamna Okowa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnonin jam'iyyar PDP guda uku sun sa labule da Obasanjo

Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwanin PDP wanda ya gudana ranar Laraba, 25 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel