Bidiyon yadda Kakakin majalisa ya duƙa kan guiwa yana gode wa gwamna bayan lashe zaɓen fidda gwanin PDP

Bidiyon yadda Kakakin majalisa ya duƙa kan guiwa yana gode wa gwamna bayan lashe zaɓen fidda gwanin PDP

  • An hangi kakakin majalisar dokokin jihar Delta a wani bidiyo ya duƙa kan guiwarsa yana mai godiya ga gwamna Okowa
  • Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen fidda gwanin PDP wanda ya gudana ranar Laraba, 25 ga watan Mayu
  • Jam'iyyar PDP ta zaɓi yan takarar gwamna da zasu fafata a babban zaɓen 2023 a mafi yawan jihohin Najeriya

Delta - Kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya duƙa kan guiwowinsa a gaban gwamna Ifeanyi Okowa, domin ya gode masa.

Daily Trust ta ruwaito cewa Kakakin majalisar ya yi haka ne bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin PDP ya zama ɗan takarar gwamna a 2023.

Kara karanta wannan

LP, NNPP, Jam’iyyu 4 da Peter Obi zai iya komawa kafin zaben 2023 bayan watsi da PDP

Zaɓen fidda gwanin PDP a Delta.
Bidiyon yadda Kakakin majalisa ya duƙa kan guiwa yana gode wa gwamna bayan lashe zaɓen fidda gwanin PDP Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, jam'iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fitar da yan takarar da zasu fafata a zaɓen gwamna da ke tafe.

Yayin zaɓen a jihar Delta, Oborevwori, ya samu kuri'u 597 daga cikin kuri'u 824 da Deleget suka kaɗa a wurin zaɓen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kalli Bidiyon anan

A zaɓen fidda gwani da jam'iyyar PDP ta gudanar jiya Laraba, ta fitar da yan takarar da zasu kare martabarta a babban zaɓen 2023 a kusan dukkanin jihohin Najeriya.

Sai dai jam'iyyar ta ɗage wasu zaɓukan zuwa yau Alhamis, bisa wasu dalilin na tsaro da yuwuwar ta da zaune tsaye.

Jihar Katsina a arewa maso yamma da jihar Neja a arewa ta tsakiya, yau Alhamis ake gudanar da zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna ƙarƙashin PDP.

A wani labarin kuma Batanci ga Annabi: Sabuwar matsala ta kunno kai a shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara

Kara karanta wannan

2023: Mataimakin Tambuwal da wasu mutum huɗu sun janye daga takara, tsohon Minista ya fice daga PDP

Mai magana da yawun Kotunan Musulunci a jihar Kano, Muzammil Ado Fagge, ya sanar da ɗage zaman shari'ar Sheikh Abduljabbar.

Ya ce ba za'a samu damar zaman Kotun ba yau saboda Alkalin da ke jagorantar Shari'ar ba shi da lafiya, sai 2 ga watan Yuni, 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel