Mataimakin Tambuwal da wasu mutum huɗu sun janye daga takara, tsohon Minista ya fice daga PDP
- A jawabin shugaban kwamitin zaɓen fidda gwanin PDP a Sokoto ya sanar da sunayen mutum biyar da suka janye daga takara
- Ya ce mataimakin gwamna Tambuwal, shugaban PDP na jiha da wasu mutum uku sun janye daga shiga zaɓen
- Sai dai ɗaya daga cikin su, Mukhtari Shagari, wanda tsohon minista ne a Najeriya ya sanar da ficewa daga PDP baki ɗaya
Sokoto - Mataimakin gwamnan jihar Sokoto da wani ɗan takarar kujerar gwamna, Muhammad Ɗan'iya, sun janye daga shiga zaɓen fidda gwanin PDP.
Shugaban kwamitin zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna karkashin PDP a zaɓe mai zuwa ne ya bayyana haka a jawabinsa kafin fara zaɓen ranar Laraba.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Shugaban kwamitin ya ce mataimakin gwamnan tare da shugaban jam'iyyar PDP na Sokoto ne suka janye daga takara.
A cewarsa, sauran waɗan da suka ɗauki matakin janyewar sun haɗa da tsohon mataimakin gwamna, Barista Mukhtari Shagari, da kuma ɗan tsohon gwamna, Sagir Bafarawa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Janyewar wacce ta zo ba zato ba tsammani ta sanya an bar tsohon Sakataren Gwamnatin jihar da ya yi murabus, Sa’idu Ubamdoma, kaɗai a matsayin ɗan takara karkashin PDP a Sokoto.
Wani tsohon minista a Sokoto ya fice daga PDP
Haka nan kuma, tsohon mataimakin gwamna a jahar, Mukhtari Shagari, ya fice daga jam'iyyar People's Democratic Party wato PDP.
Shagari, wanda tsohon ministan Albarkatun ruwa ne a Najeriya, ya sanar da haka a shafinsa na dandalin sada zumunta.
Ya ƙara da bayanin cewa nan ba da jimawa ba zai sanar wa duniya motsinsa na siyasa na gaba da jam'iyyar da zai koma don cika burinsa.
Legit.ng Hausa ta gano cewa yanzu haka ana cigaba da zaɓen fitar da ɗan takara ɗaya da zai fafata a babban zaɓen 2023 karkashin inuwar PDP.
A wani labarin na daban kuma Yan majalisar wakilai ta tarayya guda 6 sun yi amai sun lashe, sun koma PDP daga APC
Yayin da jam'iyyar APC ke ganin ta shawo kan rikicin da ya addabeta a Zamfara, wata sabuwar ɓaraka ta sake barkewa.
Yan majalisar wakilan tarayya guda 6 da suka bi gwamna zuwa APC sun lashe aman su, sun sake komawa jam'iyyar PDP.
Asali: Legit.ng