Yanzu-Yanzu: Akanta janar din jihar Ribas ya lashe tikitin gwamnan PDP
- Jam'iyyar PDP ta sabon dan takarar gwmana na zaben 2023 mai zuwa, akanta janar ne ya lashe zaben
- A yau ne jam'iyyar ke gudanar da zaben fidda gwani, wanda ake gudanarwa a fadin jihohin Najeriya
- Wannan duk dai shiri ne na babban zaben 2023 mai zuwa nan kusa, wanda 'yan Najeriya ke jiran isowarsa
Jihar Ribas - Rahoton jaridar The Nation ya tattaro cewa, Akanta-Janar na jihar Ribas, Siminialayi Fubara, ya zama dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben 2023 mai zuwa.
Fubara wanda ya fito daga karamar hukumar Opobo-Nkoro ya samu kuri’u 721 inda ya doke sauran ‘yan takara 15 inda Isaac Kamalu ya zo na biyu da kuri’u 86.
Shugaban kwamitin zabe, Farfesa Walter Mbotu neya bayyana Fubara a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani.
Dan takara Felix obua ya samu kuri'u 2, David Brigs 4, West Morgan 4, Tammy Danagogo 36 da George Kelly 37, wasu basu samu komai ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kimanin deliget 898 ne suka hallara a dakin taro na Dr. Obi Wali, wurin da aka gudanar da zaben fidda gwanin.
Mbotu ya ce daga cikin deliget 980 da ake sa ran za su kada kuri’a, 898 ne aka aminta da su, yayin da kuri’u 8 suka lalace, Daily Sun ta ruwaito.
Mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman, George Kelly da mace daya tilo, Abbie Atedoghu su ma sun halarci wurin.
Yadda aka gudanar da zaben
Bayan bayanai da Gwamna Nyesom Wike, shugabannin jam’iyyar PDP da masu neman takara suka yi, aka fara kada kuri’a da karfe 6:10 na yamma.
Kwamitin zabe ne ya kira deliget-deliget daidai da kananan hukumominsu inda suka gabatar da kuri’unsu a akwatunan zabe.
Mbotu, a baya ya yi alkawarin tabbatar da tsari na gaskiya, adalci da daidaito kamar yadda ya shawarci deliget-deliget din da su yi wa kansu adalci.
Shugaban jam'iyyar PDP, Amb. Desmond Akawor, ya ce zaben fidda gwani na gwamnan zai kawo karshen jerangiyar ayyuka na zaben ‘yan takarar jam’iyyar nan da babban zabe.
Akawor ya bayyana farin cikinsa da yadda aka yi nasarar gudanar da zabe tun daga zaben deliget zuwa na ‘yan majalisun tarayya da na ‘yan majalisun tarayya cikin aminci.
Anambra: Bayan kisan yar Arewa da 'ya'yanta 4, gwamna ya fara taka wa IPOB birki
A wani labarin, wani rahoto da jaridar Daily Trust ta fitar ya ce, gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya kafa dokar ta-baci fita a kananan hukumomi bakwai na jihar domin daukar mataki kan ayyukan IPOB ke yi.
Yankunan da abin ya shafa sun hada da Aguata, Ihiala, Ekwusigo, Nnewi ta Arewa, Nnewi ta Kudu, Orumba ta Arewa da Orumba ta Kudu.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a jihar a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng