Babu baraka a APC: Murtala Sule Garo ya karyata rade-radin sauya-sheka zuwa NNPP ko PDP
- Murtala Sule Garo ya tabbatar da cewa yana nan daram a cikin jam’iyyar APC mai mulkin Kano
- Akasin jita-jitar da ake ta yi a jihar Kano, Murtala Sule Garo ya ce bai sauya sheka zuwa adawa ba
- Tsohon Kwamishinan na kananan hukumomi ya gana da Gwamna Abdullahi Ganduje cikin dare
Kano - Alhaji Murtala Sule Garo wanda zai yi wa jam’iyyar APC mai mulki takarar mataimakin gwamna a jihar Kano ya yi magana a kan sauya-sheka.
Da ya zanta da gidan rediyon Freedom da ke Kano, Murtala Sule Garo ya tabbatar da cewa bai da niyyar canza gida a siyasa, kamar yadda ake ta yadawa.
Tsohon kwamishinan harkar kananan hukumomin ya ce yana nan tsamo-tsamo a jam’iyyar APC.
Jigon na APC a jihar Kano ya bayyana cewa a lokacin da ake magana da shi cikin tsakar dare, yana ganawa ne da Mai girma Abdullahi Umar Ganduje.
“Ƙarya ne, ni yanzu ma (ƙarfe biyu na daren Talata) ganawa muke yi da Gwamna (Abdullahi Umar Ganduje).
“Ƙarya ce kawai mutane suke yaɗawa” - Alhaji Murtala Sule Garo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta dinke a Kano
Wannan zai kawo karshen rade-radin da ke yawo cewa wanda zai yi wa APC takarar mataimakin gwamna a zaben 2023, yana neman shiga jam’iyyar NNPP.
Wasu rahotannnin kuma sun rika nuna cewa Garo zai shiga jam’iyyar hamayya ta PDP kafin zabe.
A ‘yan kwanakin nan jam’iyyar hamayya ta NNPP da ta shigo gari ta yi kasuwa sosai a Kano, ta karbi wasu daga cikin jiga-jigan da APC ta ke takama da su.
Abin da hakan yake nufi shi ne ana sa rai Murtala Garo tare da Nasiru Gawuna za su yi takarar kujerar gwamna a Kano a karkashin APC a zabe mai zuwa.
A baya an rahoto cewa Murtala Garo ya fusata da aka hana shi tikitin jam’iyyar APC mai mulki, aka zabi ya zama ‘dan takarar kujerar mataimakin gwamna.
Baya ga haka, sai da aka yi zaman sulhu da tsohon Kwamishinan domin shawo kan rikicin da ke tsakaninsa da bangaren Sanatan Arewacin Kano Barau Jibrin.
Rikicin Kano ta Arewa
A baya kun ji labarin yadda aka samu samu sabani a dalilin goyon bayan da Barau Ibrahim Jibrin ya samu na neman takarar Sanatan Arewacin Kano a APC.
A lokacin an ji cewa yaran Murtala Sule Garo ba su ji dadin sasantawar da Gwamna ya yi da Sanata Barau Jibrin ba, ya janye masa takararsa ta Sanata.
Asali: Legit.ng