Dino Melaye Ya Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa Ya Faɗi Warwawas a Zaben Fidda Gwani na PDP

Dino Melaye Ya Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa Ya Faɗi Warwawas a Zaben Fidda Gwani na PDP

  • Dino Melaye, tsohon sanata mai wakiltan Kogi West a Majalisar Najeriya ya bayyana dalilin da yasa ya sha kaye a zaben fidda gwani na PDP
  • Melaye, a wani rubutu da ya yi a shafinsa na dandalin sada zumunta ya ce wani gagarumin taron dangi aka yi masa don ganin bai kai labari ba
  • Amma, ya taya wanda ya yi nasarar, Hon Tajudeen Yusuf murna ya kuma mika godiyarsa ga wakilai da suka kada masa kuri'a a zaben na fidda gwani

Tsohon Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kogi, Dino Melaye, ya ce taron dangi da aka yi masa ne yasa ya sha kaye a zaben fidda gwani na kujerar sanata ta Kogi West karkashin jam'iyyar PDP.

The Punch ta rahoto cewa dan majalisar mai wakiltar Kabba/Bunu Ijumu, ya sha kaye a hannun Tajudeen Yusuf, inda ya samu tikitin na takarar sanata a jam'iyyar ta PDP a Kogi.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamna ya lashe tikitin PDP don sake takarar gwamna a 2023

Abin Da Yasa Na Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwani Na PDP, Dino Melaye
Dino Melaye: Abin Da Yasa Na Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwani Na PDP. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yusuf ya kayar da Melaye, wanda ya wakilci Kogi West a majalisa ta takwas da kuri'u 163 da 99.

An yi zaben raba gardamar ne a ranar Talata a Kaba bayan Melaye da TJ sun yi kunnen doki a zaben ranar Litinin.

Melaye ya taya TJ murnar nasarar da ya yi

Dino Melaye a wata wallafa da ya yi a shafinsa na sada zumunta ya taya TJ murnar nasarar samun tikitin na Kogi West.

"An fafata a zabe fidda gwanin kuma an samu wanda ya yi nasara. Ina taya Hon. T.J. Yusuf murna kuma ina godiya ga wadanda suka kada min kuri'u a zaben farko da na biyun.
"Ba karamin taron dangi aka yi min ba amma na gode wa Ubangiji. SDM.", Ya rubuta a sakon taya murnar.

Kara karanta wannan

Zaben Fidda Gwanin PDP: Bidiyon Ƙanen Fayose Suna Tiƙa Rawa Da Waƙar Zolayar Dino Melaye

A yankin Kogi West, wani tsohon ma'aikacin banki Dr Victor Adoji ne ya samu tikitin na PDP bayan yin nasara a zaben, hakan na nufin shine zai wakilci PDP a zaben na watan Fabrairun 2022.

Jonathan Ba Zai Sake Iya Yin Takarar Shugaban Kasa Ba a 2023, Falana Ya Bada Hujja

A bangare guda, Mr Femi Falana, SAN, a jiya Laraba ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ba zai iya yin takarar shugaban kasa ba a zaben 2023, Vanguard ta rahoto.

Lauya mai kare hakkin bil-adama ya ce Jonathan ba zai iya takarar ba saboda sashi na 137 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya ta 1999 (da aka yi wa gyaran fuska) kamar yadda SaharaReporters ta rahoto.

Ana ta hasashen cewa tsohon shugaban kasar zai iya fice wa daga jam'iyyar PDP ya koma APC gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel