Da dumi-dumi: Gwamnonin APC sun shirya tsaf domin zaban dan takarar shugaban kasa
- Gwamnonin APC sun amince da matakin da jam’iyyar ta dauka na gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a maimakon yin ittifaki kan dan takara
- Joe Igbokwe, jigo a jam’iyyar kuma mai goyon bayan tafiyar takarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne ya bayyana hakan
- Gwamnonin sun ce suna son a gudanar da sahihin zabe da tantancewa ga duk masu neman tsayawa takara da suka saya kuma suka mika fom din tsayawa takara
Najeriya - Wani rahoto da ke fitowa ya nuna cewa gwamnonin Najeriya a karkashin jam’iyyar APC sun amince da zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a gudanar kafin babban zaben 2023.
Joe Igbokwe, jigo a jam’iyyar APC wanda ya bayyana hakan, ya fadi a ranar Talata, 24 ga watan Mayu, cewa gwamnonin sun ba da cikakken goyon baya ga duk wani mai neman tsayawa takarar shugaban kasa domin nuna bajintarsa cikin gaskiya da adalci.
Wannan magana dai ta fito ne bayan wata tattaunawa ta sirri da gwamnonin jam’iyyar mai mulki suka yi, kamar yadda rahotanni suka bayyana a baya.
Igbokwe ya rubuta a Facebook cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gwamnonin APC sun bayyana goyon bayansu ga zaben fidda gwani na shugaban kasa da za a gudanar, tare da baiwa duk wani wanda ya sayi fom din tsayawa takarar shugaban kasa damar yin takara cikin gaskiya da adalci."
Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba
A baya kun ji cewa, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Asabar din da ta gabata, ya ce bai damu da zama abokin tafiyar wani dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2023 mai zuwa.
An ambaci sunan Zulum a cikin wasu batutuwan siyasa a matsayin wanda ka iya zama abokin jiko na gari ga dan takarar shugaban kasa na APC, Premium Times ta ruwaito.
Zulum ya yi maganar ne a lokacin da ya karbi bakuncin tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi, wanda ya je Borno domin ganawa da deliget din APC na jihar gabanin zaben fidda gwani na ranar 29 ga watan Mayu.
Gwamna Zulum, wanda ya yaba wa kwarjinin Amaechi, ya ce bisa ka’idarsa, ba ya goyon bayan duk wani mai son tsayawa takara saboda imaninsa cewa Allah ne ke bayarwa kuma yake hana mulki.
A wani labarin, na daban, jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba wasa yake ba a burinsa na zama shugaban kasa, ya kara da cewa al’ummar kasar nan na bukatar shugaban da zai kawo sauyi irin sa a 2023.
Tinubu wanda ya je Benin, babban birnin jihar Edo a karshen mako domin neman bakin wakilan APC gabanin fidda gwani, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Oba na Benin a fadarsa.
A cewar Tinubu: "Ni ne wanda ya fi cancanta da dacewa na tsayawa takarar shugaban kasa da kuma jagorantar al'ummar kasar nan wajen magance matsalolin tattalin arziki da tsaro."
Asali: Legit.ng