Yana Sanatan APC amma sunan Danjuma Goje ya bayyana wajen zaben fidda gwanin PDP

Yana Sanatan APC amma sunan Danjuma Goje ya bayyana wajen zaben fidda gwanin PDP

  • Deleget sun yi mamaki yayinda suka ga sunan Sanata Danjuma Goje cikin yan takara a zaben fidda gwani
  • Sanata Danjuma Goje dai yana wakiltan mazabar Gombe ta tsakiya a majalisar dattijan tarayya
  • Tsohon gwamnan na jihar Gombe har ila yau dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ne

Gombe - Wakilan zaben shugaba wadanda akafi sani da deleget na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe sun ga abin mamaki ranar Litnin wajen zaben fidda gwani.

Yayinda suka shiga kada kuri'unsu, sai suka ga Sanatan APC mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje, cikin jerin yan takaran, rahoton Leadership.

Zaku tuna cewa an yi rade-radin Sanata Danjuma Goje zai sauya sheka daga APC zuwa PDP sakamakon rashin jituwar dake tsakninsa da Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

Tuni dai uwar jam'iyyar APC ta shirya zaman sulhu tsakanin jiga-jigan siyasan kuma hakan ya hana Danjuma Goje komawa PDP.

Amma a ranar Litinin yayi zaben fidda gwanin PDP, sunan Danjume Goje ya bayyana cikin yan takara.

Amma bayan kada kuri'ar, Goje bai samu kuri'a ko guda ba inda Abubakar Aliyu ya lashe zaben da kuri'u 59.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Danjuma Goje
Yana Sanatan APC amma sunan Danjuma Goje ya bayyana wajen zaben fidda gwanin PDP Hoto: Leadership
Asali: Facebook

N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai

Matasa da mata 2,200 a Gombe ne Sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya a majalisar dattawa ta kasa, Sanata Danjuma Goje ya ba tallafin sana'a.

Legit.ng ta samo cewa, Goje, wanda tsohon gwamnan jihar Gombe ne ya raba musu makudan kudade a matsayin jarin fara kasuwancin da suka iya a ranar Litinin, 29 ga watan Maris.

Daga cikin mutane 2,200 da suka ci gajiyar shirin karfafawar ta Sanata Goje, 1000 matasa maza ne yayin da 1,200 kuma mata ne, wadanda dukkansu sun fito ne daga kananan hukumomin Yamaltu-Deba da Akko.

Kara karanta wannan

Tikitin shugaban kasa na PDP: Ina addu’a Allah yasa Wike ya kai labari – Okezie Ikpeazu

Ko da yake ba a fayyace gudunmawar ta kudaden da aka bai wa mata 1,200 ba, kowanne daga cikin matasan ya samu Naira 30,000, wanda jumillarsu ya kai Naira miliyan 30.

Matasa 1,000 ne aka zaba kana aka horar da su sana’o’i daban-daban daga Hukumar Kula da Ayyukan yi ta kasa (NDE), don samun dogaro da kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng