Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba

Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba

  • Gwamnan jihar Borno ya bayyana cewa, ba tsayawa takara bane a gabansa, face aikin da yake yi a jiharsa ta Borno
  • Ya bayyana haka ne yayin da ministan sufuri Amaechi ya kai masa ziyarar neman goyon baya a fadarsa ta jihar
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa, Allah ne ke ba da mulki, kana ba zai zabi dan takara ba a bisa ka'idar rayuwarsa

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, a ranar Asabar din da ta gabata, ya ce bai damu da zama abokin tafiyar wani dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC mai mulki a zaben 2023 mai zuwa.

An ambaci sunan Zulum a cikin wasu batutuwan siyasa a matsayin wanda ka iya zama abokin jiko na gari ga dan takarar shugaban kasa na APC, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

Gwamnan jihar Borno, Zulum ya magantu game da batun takara
Ba zan roki kowa ya bani matsayin mataimakin shugaban kasa ba – Gwamna Zulum | Hoto: leadership.ng
Asali: Twitter

Zulum ya yi maganar ne a lokacin da ya karbi bakuncin tsohon ministan sufuri, Chibuike Amaechi, wanda ya je Borno domin ganawa da deliget din APC na jihar gabanin zaben fidda gwani na ranar 29 ga watan Mayu.

Gwamna Zulum, wanda ya yaba wa kwarjinin Amaechi, ya ce bisa ka’idarsa, ba ya goyon bayan duk wani mai son tsayawa takara saboda imaninsa cewa Allah ne ke bayarwa kuma yake hana mulki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Meye martanin gwamna Zulum?

Ya ce a matsayinsa na jagora a jihar Borno, zai yi aiki da duk wani shugaban da Allah ya ba shi damar zama shugaban kasar Najeriya.

Zulum ya ce, idonsa a bude yake wajen karbar duk masu neman takarar shugabancin kasar nan a APC, domin ba shi da wani buri na musamman, in ban da aikin da yake yi a yanzu.

Kara karanta wannan

Sarkin Katsina ga Osinbajo: Muna bayanka, Ina addu'ar ka yi nasarar gaje Buhari

Amaechi, ya kai ziyarar ne Maiduguri tare da Sanatoci biyu, Ali Ndume da Ayogu Eze, tsohon babban hafsan soji, Tukur Buratai, da sauran jami’ai, rahoton The Guardian.

A bangarensa, ya shaida wa wakilan APC cewa idan aka zabe shi a matsayin dan takara, zai habaka tsaron Najeriya tare da bunkasa fannin noma da inganta harkokin sufuri da samar da wutar lantarki.

Ya kuma yi alkawarin sake waiwayo da akalar ayyukansa ga aikin hakar mai a yankin Arewa maso Gabas.

2023: Da gaske fa nake ina son gaje Buhari, cewar Tinubu ga sarakunan gargajiya

A wani labarin, na daban, jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ba wasa yake ba a burinsa na zama shugaban kasa, ya kara da cewa al’ummar kasar nan na bukatar shugaban da zaai kawo sauyi irin sa a 2023.

Tinubu wanda ya je Benin, babban birnin jihar Edo a karshen mako domin neman bakin wakilan APC gabanin fidda gwani, ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga Oba na Benin a fadarsa.

Kara karanta wannan

2023: Buhari Muke Jira Ya Faɗa Wanda Ya Ke Son a Ba Wa Takarar Shugaban Ƙasa, Mu Yi Biyayya, Zulum

A cewar Tinubu: "Ni ne wanda ya fi cancanta da dacewa na tsayawa takarar shugaban kasa da kuma jagorantar al'ummar kasar nan wajen magance matsalolin tattalin arziki da tsaro."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.