Janar Buratai ya roki ‘Yan APC su zabi Amaechi, Gwamna Zulum bai bada goyon baya ba
- Janar Tukur Yusuf Buratai ya yi wa Rotimi Amaechi rakiya da ya gana da ‘Yan APC a jihar Borno
- Tsohon hafsun sojojin na kasa ya roki mutanensa su marawa Amaechi baya a zaben tsaida gwani
- Gwamna Babagana Zulum ya fadawa ‘yan APC su zabi wanda ya dace, ya roki Allah da ya yi zabi
Borno - Tsohon shugaban sojojin kasa, Tukur Yusuf Buratai, ya yi kira ga ‘ya ‘yan APC su zabi Rotimi Amaechi a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa.
The Cable ta ce Janar Tukur Yusuf Buratai mai ritaya ya yi wannan roko ne sa’ilin da suka ziyarci jihar Borno domin nemawa Rotimi Amaechi goyon baya.
Tsohon hafsun da yanzu ya zama Ambasadan na Najeriya zuwa kasar Benin ya yi bayani a gaban ‘ya ‘yan jam’iyyar APC masu zaben ‘dan takara a 2023.
Da yake jawabi a ranar Lahadi, 22 ga watan Mayu, 2022, Janar Tukur Buratai ya yabi Rotimi Amaechi a matsayin mutum mai jajircewa da karfin hali.
The Nation ta ce Buratai ya fadawa taron na jam’iyyar APC mai mulki cewa tsohon gwamnan na jihar Ribas yana da duk abin da ake bukata wajen rike Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jawabin Janar Tukur Yusuf Buratai
“Mai girma, ba za mu raba kuri’unmu ba. A bada 100% na kuri’unmu ga Rotimi Amaechi. Zan fada maku dalilin da ya sa na fadi haka.”
“Mu na tare da mutumin da ya shirya shugabanci, ya kuma nuna jajircewarsa da kwarewa a aiki a mukaman da ya rike a shekarun nan.”
- Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd)
Tsohon Hafsun kasan sojan ya ce Amaechi ya rike kujerar shugaban majalisa, ya zama gwamnan jiha a Ribas, sannan ya zama Minista a gwamnatin tarayya.
"Ya jagoranci abokan aikinsa gwamnonin jihohi sau biyu. Ya kuma jagoranci takwarorinsa a matsayin shugaban majalisun dokoki.”
“Ya na da sanin aiki, sannan kuma mafi muhimmanci, ya rike amanar Muhammadu Buhari.”
- Janar Tukur Yusuf Buratai (rtd)
Kafin Amaechi ya yi jawabi, Buratai ya tunawa mutanen Borno cewa an san su da nasara, don haka su yi watsi da kowa su zabi tsohon Ministan a zaben APC.
Zulum ya ce Allah ke bada mulki
Rotimi Amaechi ya yi kira ga ‘yan jam’iyya su ba shi kuri’arsu domin ya zama ‘an takara. Amma sai aka ji Gwamna Babagana Zulum ya na wani kira na dabam.
An ji Gwamnan na Borno ya ba masu zaben ‘dan takara shawara su yi amfani da tunaninsu wajen tsaida wanda ya cancanta, tare da sanin mulki na Ubangiji ne.
Farfesa Zulum bai nuna za a zabi Amaechi a jihar Borno ba, sai dai ya yi addu’a a samu shugaba na gari, ya kuma ce za su saurari umarnin shugaban kasa Buhari.
Asali: Legit.ng