2023: 'Yan kwamiti sun haramtawa tsohon Sanatan PDP shiga zaben neman Gwamna a APC
- ‘Yan kwamitin da aka nada domin tantance ‘Yan takaran Kuros Ribas sun kawowa Bassey Otu cikas
- Da alama Sanata Bassey Otu ba zai iya neman kujerar Gwamna a APC ba saboda matsalar takardu
- Gwamna Ben Ayade yana goyon bayan tsohon Sanatan ya gaje shi, amma an kai wa APC korafi a kansa
Cross River - Kwamitin da ke tantance ‘yan takarar jam’iyyar APC a jihar Kuros Riba, ya haramtawa Sanata Bassey Otu shiga zaben gwamna a 2023.
Kamar yadda labari ya je wa jaridar nan ta The Cable, Sanata Bassey Otu ba zai iya shiga zaben fitar da gwanin zama ‘dan takarar gwamna a Kuros Ribas ba.
Ana tunani an hana ‘dan siyasar yin takara a jam’iyyar ta APC mai mulki ne saboda ya gagara kawowa kwamitin takardar kammala firamare da na WASC.
Shugaban kwamitin na APC, sakatarensa da wani ‘dan kwamitin; Suleiman Fakai, Chidi Nwogu da Paul Oyiborume sun sa hannu wajen daukar matakin nan.
An kai wa kwamitin Fakai korafi
Suleiman Fakai, Chidi Nwogu da Paul Oyiborume sun ce sun samu korafi a ranar 14 ga watan Mayu daga Messrs B.I Dakum & Co game da takarar Sanata Otu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Masu korafin su na ikirarin an taba daure Bassey Ede Otu, sannan bai iya gabatar da shaidar karatunsa ba. Amma ba wannan korafin ya rusa masa takara ba.
‘Yan kwamitin sun ce bayan gudanar da bincike da kyau a kan bayanan korafin da hujjojin da aka gabatar, ba a samu wani abin da ya gaskata zargin da ake yi ba.
Babu takardar firamare da WASC
Sai dai wanda ake tuhuma da laifin bai biya gabatar da takardar kammala makarantar firamare ba, haka zalika ba a iya ganin shaidar jarrabawar WASC dinsa ba.
Kwamitin ya ce Otu ya kawo shaidar yin karatu a makarantar sakandare a madadin satifiket ne. A karshe wannan ta sa aka dakatar da batun neman takararsa.
Ayade yana tare da Otu
Jaridar Sahara Reporters ta ce Otu shi ne wanda Mai girma gwamna Ben Ayade yake so ya yi wa jam’iyyar APC mai mulki takarar gwamna a zaben shekarar badi.
Farfesa Ben Ayade ya zabi tsohon ‘dan majalisar a matsayin wanda zai nemi ya maye gurbinsa. 'Dan siyasar ya yi shekaru 12 a majalisar wakilai da na dattawa.
Bello El-Rufai zai samu tikitin APC?
Ana da labari Hon. Samaila Suleiman ya bar APC zuwa PDP. Kun samu rahoto cewa gaskiyar abin da ya faru shi ne ‘Dan majalisar na Kaduna ba zai samu tikitin APC ba.
Alamu masu karfi sun nuna Bello El-Rufai ne wanda jam'iyyar APC za ta ba takara a yankin Kaduna ta Arewa, hakan ta sa Suleiman ya zabi ya jarraba sa'a a PDP.
Asali: Legit.ng