2023: Fayemi na da kwarewar iya aiki da zai iya shugabancin Najeriya, Ortom

2023: Fayemi na da kwarewar iya aiki da zai iya shugabancin Najeriya, Ortom

  • Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce shugaban NGF kuma gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya cancanta ya mulki Najeriya
  • Ortom na jam'iyyar PDP ya yaba wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ne yayin da ya karɓi bakuncinsa a fadar gwamnati ranar Asabar
  • Da yake jawabi, Fayemi ya ce zai gyara hukumomin tsaro da kuma karfafa amfani da fasaha wajen magance kalubalen tsaro

Benue - Gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya ce takawaransa na jihar Ekiti, Gwamna Kayode Fayemi, na da kwarewar da zai shugabanci Najeriya.

Gwamna Ortom na jam'iyyar PDP ya yi wannan furucin ne yayin da ya karɓi bakuncin Feyemi, ɗan takarar shugaban kasa a APC, a gidan gwamnatin Benuwai ranar Asabar.

Gwamna Ortom tare da gwamna Fayemi.
2023: Fayemi na da kwarewar iya aiki da zai iya shugabancin Najeriya, Ortom Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

The Cable ta rahoto cewa Fayemi ya je jihar ne domin shawari da masu ruwa da tsaki na jami'iyyar APC a Benuwai gabanin zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya faɗi sunan ɗan takarar da zasu zaɓa a zaɓen fidda magajin Buhari na APC

Sakataren watsa labari na gwamna Ortom, Nathaniel Ikyur, a wata sanarwa ya jiyo Uban Gidansa na cewa ba tare da duba addini ko siyasa ba, dukkan yan Najeriya na fatan warware kwalubalen da ya dabaibaye ƙasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamna Ortom ya ce:

"Dukkan mu mun shiga ciki kuma akwai bukatar mu haɗa kai mu yi aiki tare mu ceto ƙasar mu."

Gwamnan ya yaba wa dukkan masu sha'awar shugabancin ƙasa, inda ya ƙara da cewa duk wanda mutane suka zaba ya kamata ya fifita Najeriya fiye da bukatun zuciyarsa.

Zan dawo da zaman lafiya a ƙasa - Fayemi

A ɓangarensa, gwamna Fayemi ya ce da zaran ya ɗare mulkin Najeriya zai gyara hukumomin tsaro da kayan aiki, gami da ƙarfafa amfani da fasaha wajen shawo kan matsalar tsaro.

Ɗan takarar kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin ƙasa NGF, ya ce zai shawo kan talaucin da ya addabi yan ƙasa, wanda a ganinsa shi ya haddasa rashin tsaro.

Kara karanta wannan

2023: APC ko PDP duk wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa zan taya shi murna, Hadimar Buhari

A wani labarin na daban kuma Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom

Tsohon ɗan majalisar tarayya , Dakta Usman Bugaje, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe.

Tsohon hadimin Atiku Abubakar ɗin ya ce Najeriya ta tsaya cak tana bukatar jajirtattun shugabanni a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel