Zaɓen fidda gwanin APC: Gaba ɗaya kuri'un mu naka ne, Lalong ga Amaechi

Zaɓen fidda gwanin APC: Gaba ɗaya kuri'un mu naka ne, Lalong ga Amaechi

  • Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce baki ɗaya Deleget ɗin jihar tsohon ministan Sufuri zasu kaɗa wa kuri'un su
  • Lalong yace mutanen jihar Filato da shi karan kansa ba zasu taba mancewa da abin da ɗan takarar shugaban ƙasan ya musu ba
  • Ya ce duk wani aiki da ya zuba wa al'ummar jiharsa ta Filato ya koya ne daga wurin, Amaechi, dan haka ya sha kuruminsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jos, Plateau - Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya ce baki ɗaya Deleget din jihar zasu zaɓi tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, a zaɓen fidda ɗan takarar APC da ke tafe.

Lalong ya yi wannan furucin ne yayin ganawa da Amaechi da Deleget ɗin APC a fadar gwamnatinsa da ke Jos, ranar Jumu'a, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom

Amaechi da Lalong.
Zaɓen fidda gwanin APC: Gaba ɗaya kuri'un mu naka ne, Lalong ga Amaechi Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnan ya ce:

"Kai ne ɗan takarar shugaban ƙasa na farko da ka zo ganin mu, duk wanda na gayyata sai ya noƙe, ya faɗa mun zai ɓata lokacinsa ne saboda Mutanen Filato ba zasu zaɓe su ba, Amaechi ne na su."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Saboda haka ba bukatar sai ka yi dogon jawabi, muna fatan mu dogara da wanda ya yi aka gani. Muna gaya maka haka ne saboda kar ka ɓata lokaci wajen zuwa Kamfe, mun yanke hukunci don ka yi wa mutanen mu."
"Ka taimakawa kowace jiha a arewa ta yi rijustar jam'iyyar APC kuma muka sabunta Rijista, lokacin da muka dawo neman tazarce a Filato kowa gudun mu ya yi, amma kai ka tsaya mana."

Wane tagomashi Amaechi ya kai Filato?

Gwamna Lalong ya kara da cewa lokacin da ya sake tsayawa takara tsohon ministan ne ya yi ruwa ya yi tsaki har ya cimma nasara.

Kara karanta wannan

2023: APC ko PDP duk wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa zan taya shi murna, Hadimar Buhari

A cewarsa tsohon gwamnan Ribas din ya goyi bayan su tare da yan majalisun jiha da dama yayin da kowa ya guje su.

"Duk ayyukan da nake yi daga wurin ka na gani, muna godiya da zuwanka. A jihar Filato zamu baka ƙarfi, gwarin guiwa kuma muna alfaharin faɗin haka a ko ina."

A wani labarin kuma Tsohon ɗan majalisa ya ayyana shiga takarar shugaban ƙasa a 2023, Ya lale kuɗi ya sayi Fom

Tsohon ɗan majalisar tarayya , Dakta Usman Bugaje, ya shiga tseren takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 da ke tafe.

Tsohon hadimin Atiku Abubakar ɗin ya ce Najeriya ta tsaya cak tana bukatar jajirtattun shugabanni a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel