APC ko PDP duk wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa zan taya shi murna, Onochie

APC ko PDP duk wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa zan taya shi murna, Onochie

  • Hadimar shugaban ƙasa Buhari ta fannin Midiya, Lauretta Onochie, ta ce kowaye INEC ta sanar ya ci nasara zata yi masa murna
  • Onochie ta bayyana cewa ba ta damu da ɗan wane yanki ko jam'iyya bane, burinta a samu mai kishin ƙasa kamarta
  • A baya dai an sha cece kuce lokacin da shugaba Buhari ya sanya sunanta cikin kwamishinonin INEC da ya aike wa Majalisa

Abuja - Mai taimakawa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan harkokin kafafen sada zumunta, Lauretta Onochie, a ranar Alhamis, tace ba ta damu da tsarin karɓa-karɓa ba matukar za'a zaɓi shugaba nagari.

Punch ta ruwaito hadimar Buharin na cewa a shirye take duk wanda ya samu nasarar lashe zaɓe zata taya shi murna, ɗan APC ne ko ɗan PDP.

Kara karanta wannan

Ana shirin tukarar zaben 2023, Tsohon Ministan Buhari ɗan takara ya fice daga jam'iyyar APC

Lauretta Onochie
APC ko PDP duk wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa zan taya shi murna, Onochie Hoto: Punchng.com
Asali: Depositphotos

Ta ce:

"Kowane mutum ne jam'iyyar APC ko PDP ta tsayar takara kuma ya samu nasara a zaɓe, zan taya shi murna."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ban da mu da waye zai zama shugaban ƙasa na gaba ba, daga wane yankin zai fito, matukar ya kasance mai kishin ƙasa kamar yadda nike da kishi."

An cire sunan Hadimar shugaban ƙasa daga jerin sunayen da Buhari ya naɗa a matasayin kwamishiniyar INEC mai wakiltar Delta kuma aka maye gurbinta da May Agbamuche Mbu.

Hakan ta faru ne bayan yan Najeriya sun yi raddi ga gwamnatin shugaba Buhari, bisa zargin tana da tsagin da ta ke mutuwar so a siyasa.

Ni ba yar jam'iyyar APC bace - Onochie

Da take kare kanta kan wannan zargin a bayan, Onochie ta koka kan cewa da wahala ka iya wa ɗan Najeriya.

Kara karanta wannan

Jerin yan takarar shugaban ƙasa a APC da suka sayi Fom N100m kuma suka gaza maida wa

"Na faɗi gaskiya amma suna tsammanin kowa irin su ne, mutane na ganin ƙarya nike lokacin da nace ni ba mamba bace a APC, kuma har yanzun ina kan bakata ni ba mamba bace."

Onochie ta shafe shekara 16 tana aikin koyarwa a Burtaniya kafin daga bisani a naɗa ta mai taimakawa shugaban ƙasa a fannin midiya.

A wani labarin nadaban kuma Jerin yan takarar shugaban ƙasa a APC da suka sayi Fom N100m kuma suka gaza maida wa

Jam'iyyar All Progressive Congress APC ta bayyana sunayen yan takarar shugaban ƙasa da suka sayi Fom miliyan N100 kuma suka gaza cikewa su mayar .

Idan masu bibiyan mu ba su manta ba jam'iyyar APC mai mulki ta saka N30m a matsayin kudin Fom ɗin nuna sha'awa da kuma miliyan N70m kuɗin Fom ɗin tsayawa takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel