Kakakin Buhari, Femi Adesina, Ya Bayyana Sana'ar Da Zai Fara Bayan Shugaban Ƙasar Ya Sauka Daga Mulki a 2023

Kakakin Buhari, Femi Adesina, Ya Bayyana Sana'ar Da Zai Fara Bayan Shugaban Ƙasar Ya Sauka Daga Mulki a 2023

  • Femi Adesina, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman akan harkokin yada labarai ya ce zai koma gona bayan mulkin Buhari
  • Adesina ya bayyana hakan ne ta wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook bayan ya amshi ziyarar Kungiyar Manoman Najeriya, reshen Jihar Edo a ofishinsa
  • Kamar yadda ya ce idan ya gama aiki da gwamnatin tarayya, ya na da burin ci gaba da harkar labarai da kuma noma da yardar Ubangiji

Abuja - Hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a harkar yada labarai, Femi Adesina, ya bayyana burinsa na zama manomi bayan wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare.

Daily Trust ta ruwaito cewa Adesina ya yi wannan bayanin ne ta wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook yayin da ya amshi ziyarar Kungiyar Manoman Najeriya, reshen Jihar Edo a ofishinsa.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran NNPP da ya bi Ganduje, ya janye jiki ya dawo Kwankwasiyya bayan awa 24

Kakakin Buhari, Femi Adesina, Ya Bayyana Sana'ar Da Zai Fara Bayan Buhari Ya Sauka Daga Mulki
Femi Adesina, Ya Bayyana Sana'ar Da Zai Fara Bayan Buhari Ya Sauka Daga Mulki. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, Adesina ya ce:

“Idan na gama da wannan gwamnatin, da yardar Ubangiji ina da niyyar komawa harkar ayyukan yada labarai kuma ina so in zama manomi. Ina fatan Ubangiji ya cika min burina.
“Na yi mamakin ganin kungiyar manoman Najeriya (Reshen Jihar Edo) su na min tayin majibancinsu. Na tambayi kai na: ‘Ya aka yi su ka san ina da niyyar fara noma? Kila sun hango gobe ne.”

Adesina ya yi ayyuka da jaridu daban-daban

Adesina ya fara harkar yada labarai inda ya yi aiki da jaridar Vanguard kafin ya koma aiki da jaridar National Concord.

Har ila yau ya zama zakara cikin ma’aikatan jaridar The Sun a matsayin mai tace labarai daga baya ya zama manajan darekta sannan kuma ya zama shugaban banagaren tace labarai na gidan jaridar.

Kara karanta wannan

Daga Ƙarshe, Adesina Ya Yi Magana Kan Batun Takarar Shugaban Ƙasa a 2023

A shekarar 2015 ya fara aiki da shugaban kasan Najeriya a matsayin hadiminsa na musamman na harkokin yada labarai.

Ba a Taɓa Gwamnatin Da Ta Kai Ta Buhari Rashawa Ba: Naja'atu Ta Ragargaji Buhari Kan Yafewa Dariya Da Nyame

A wani rahoton, Naja’atu Mohammed, mamba a Hukumar Dauka da Ladabtar ‘Yan sanda, PSC, ta caccaki Shugaban Kasa Muhammadu Buhari akan yafe wa tsofaffin gwamnoni, Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.

Daily Nigerian ta ruwaito yadda a ranar Alhamis, majalisar jiha, wacce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta ta yafe wa Dariye da Nyame tare da wasu fursinoni 157 da ke fadin kasar nan.

An yanke wa Dariye, wanda ya rike kujerar gwamnan Jihar Filato tsakanin 1999 da 2007, shekaru 14 a gidan yari saboda satar N1.16b, sannan an yanke wa Nyame shekaru 12 a gidan yari akan satar N1.6b, wanda ya yi gwamnan Jihar Taraba tsakanin 1999 da 2007 a shekarar 2020.

Asali: Legit.ng

Online view pixel