Atiku ya lissafa jihohi 5 da yake zargin APC ta sace masa kuri’u a 2019
- Gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na PDP, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bukaci wakilan jam’iyyar su zabe shi
- Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa jam’iyyar APC ta sace masa kuri’unsa a jihohin Katsina, Kano, Yobe, Kaduna da Borno a 2019
- Dan siyasar na magana ne a kan zaben da ya sha kaye a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Katsina - Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya jadadda cewa lallai an yi magudi ne a zaben shugaban kasa na 2019 wanda ya sha kaye a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Atiku wanda ke sake neman takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya yi zargin ne a lokacin da ya gana da wakilan jam’iyyar a jihar Katsina, Vanguard ta rahoto.
Legit Hausa ta zakulo jerin jihohi biyar da dan siyasar wanda ya kasance haifaffen jihar Adamawa ya zargi APC da sace masa kuri’u, ga su kamar haka:
1. Jihar Katsina
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Jihar Kano
3. Jihar Kaduna
4. Jihar Borno
5. Jihar Yobe
Kada ku bari a sace mun kuri’una a 2023, Atiku ya roki deleget din Katsina
Koda dai Atiku bai riga ya mallaki tikitin shugaban kasa na PDP na 2023 ba, ya bukaci deleget din Katsina da kada su bari a sake sace masa kuri’unsa a zabe mai zuwa.
Ya roki deleget din da su tsaya masa sannan kada su yi watsi da shi a zaben fidda gwani mai zuwa.
Ya ce:
“A zaben 2019, jihar Katsina na cikin jihohin da APC suka yi magudin sakamakon zabe. Sun kuma sace mana sakamako a jihohi hudu: Kano, Kaduna, Borno da Yobe.
“Don haka, ina godiya ga mutanen jihar Katsina kan goyon bayan da suka ba PDP kuma ina fatan a wannan karon ba za ku bari a sace kuri’unku ba.”
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma bayyana cewa al’ummar Katsina na goyon bayan sa a kodayaushe, inda ya kara da cewa al’ummar jihar Arewa maso yamma ne suka horas da shi a fagen siyasa.
2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka
A wani labarin, wani dan takarar gwamna a jihar Plateau, Ambasada Yohana Margif, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Margif, wanda ya siya fom din takara na zaben gwamna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a cikin wata sanarwa da ya saki ga manema labarai a garin Jos, a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu, jaridar Punch ta rahoto.
Har ila yau, ya sanar da hukuncin da ya yanke a cikin wata wasika wanda aka gabatawar shugaban APC na gundumar Margif/Kopmur da ke Mushere, karamar hukumar Bokkos, wadda aka mika kwafinta ga shugabannin APC na karamar hukuma da na jaha.
Asali: Legit.ng