2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka

2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka

  • Dan takarar gwamna na APC a jihar Plateau, Ambasada Yohana Margif, ya janye daga tseren duk da cewar ya siya fom din naira miliyan 50
  • Margif ya kuma fice daga jam’iyyar mai mulki saboda zargin tursasa wani dan takara da bai da farin jini, yana mai cewa APC ta rushe a jihar
  • Ya kuma ce ya sadaukar da kudin fom da ya biya domin ayi amfani da shi wajen bunkasa damokradiya a jihar, Najeriya da Afrika baki daya

Plateau - Wani dan takarar gwamna a jihar Plateau, Ambasada Yohana Margif, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Margif, wanda ya siya fom din takara na zaben gwamna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar a cikin wata sanarwa da ya saki ga manema labarai a garin Jos, a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka
2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka Hoto: Government of Plateau State, The State of Plateau
Asali: Facebook

Har ila yau, ya sanar da hukuncin da ya yanke a cikin wata wasika wanda aka gabatawar shugaban APC na gundumar Margif/Kopmur da ke Mushere, karamar hukumar Bokkos, wadda aka mika kwafinta ga shugabannin APC na karamar hukuma da na jaha.

A wasikar mai kwanan wata 17 ga watan Mayun 2022, Ambasada Yohana Margif ya koka kan rugujewar damokradiyar cikin gida a jam’iyyar APC ta jihar Filato da tursasa dan takara mara farin jini a matsayin dalilinsa na sauya sheka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai taimakon jama’ar ya ce ayi amfani kudin da ya biya na siyan fom din APC a matsayin nasa gudunmawar don bunkasa damokradiyya a jihar Filato, Najeriya da Afrika baki daya ba wai ga APC ba.

Ya kuma bayyana cewa lallai gadar APC a jihar Filato ya karye kuma ya rushe gaba daya, rahoton Thisday.

Kara karanta wannan

APC da PDP sun fi karfin talaka da matasa: Adamu Garba ya sayi fom din takara a YPP

Sanarwar tasa na zuwa ne kwanaki biyu bayan jam’iyyar mai mulki ta kammala tantance yan takararta na zaben gwamna a fadin kasar.

Sai dai kuma ya yi biris a kan sabuwar jam’iyyarsa.

2023: 'Yan takarar gwamnan APC a Filato sun yi baranzanar sauya sheka saboda dalilai

A baya mun ji cewa dukkanin yan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Filato sun yi barazanar ficewa daga jam’iyyar idan ba a bi tsarin da ya dace ba wajen zabar wanda zai rike tutar ta ba.

Shugaban kungiyar yan takarar gwamnan APC, Cif Amos Gizo, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, a taron manema labarai a sakatariyar jam’iyyar ta jihar, rahoton The Guardian.

Gizo, wanda ya kasance dan takarar gwamna, ya bayyana cewa duk wani yunkuri na Gwamna Simon Lalong na tursasa dan takara kan jam’iyyar da mutanen Filato zai fuskanci turjiya.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng