Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida ne ɗan takarar gwamnan Kano karkashin NNPP a 2023

Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida ne ɗan takarar gwamnan Kano karkashin NNPP a 2023

  • Jam'iyya mai tashe a Kano wato NNPP me kayan marmari ta tsayar da Abba Kabir Yusuf a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano
  • Fitaccen ɗan siyasan ya yi kaurin suna a bakin mutane saboda wakar da aka masa mai take Abba Gida Gida
  • Tshon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ne ɗan takara a Kano ta tsakiya, NNPP ta jero sauran yan takararta a Kano

Kano - Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari ta yarda cewa Abba Kabir Yusuf, wato Abba Gida-Gida ya zama ɗan takararta na gwamnan jihar Kano a zaɓen 2023.

Daily Trust ta tabbatar da cewa NNPP ta amince Abba Gida-Gida da abokin takararsa a 2019, Aminu Abdussalam, su kare martabar jam'iyyar a zaɓen dake tafe.

Abba Kabir Yusuf.
Da Dumi-Dumi: Abba Gida-Gida ne ɗan takarar gwamnan Kano karkashin NNPP a 2023 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sun yi ƙaurin suna ne a bakunan mutane tare da fitacciyar wakar nan ta siyasa, 'Abba Gida-Gida' lokacin da suka fafata da gwamna Ganduje a zaben 2019 wanda daga baya aka bayyana da bai kammalu ba.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon MD na NDDC kan zargin handamar N47bn

Sauran yan takarar NNPP a Kano

Jam'iyyar ta kuma miƙa tikitin takarar sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya hannun tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, wanda ya koma NNPP a hukumance ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran waɗan da NNPP ta duba yuwuwar ba su tikitin takarar sanata sune tsohon Sakataren TETFund, Abdullahi Baffa a Kano ta arewa, sai kuma tsohon hadimin shugaban ƙasa kan harkokin Majalisa,, Kawu Sumaila, wanda zai nemi Kano ta kudu.

Kwafin takardar yan takarar da jam'iyyar ta amince da su, wanda gidan jaridar ya ci karo da shi, ya nuna sauran yan takara da ta cimma matsaya 36 cikin mazaɓun majalisar dokokin tarayya 40 na jihar Kano.

A wani labarin kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bi Shekarau har gida, ya ba shi takarar Sanatan da ta canza lissafin 2023

Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel