Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon MD na NDDC kan zargin handamar N47bn

Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon MD na NDDC kan zargin handamar N47bn

Jami'an hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, a ranar Laraba sun yi ram da tsohon manajan daraktan hukumar cigaban Neja Delta, NDDC, Nsima Ekere.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ana zargin tsohon shugaban hukumar NDDC din da waskar da makuden kudade da suka kai N47 biliyan ta hanyar amfani da 'yan kwangila masu rijista na hukumar.

Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwajaren ne ya tabbatar wa da Channels TV hakan.

Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon MD na NDDC kan zargin handamar N47bn
Da duminsa: EFCC ta yi ram da tsohon MD na NDDC kan zargin handamar N47bn. Hoto daga channelstv.com
Asali: UGC

Karin bayani na nan tafe...

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel