Yanzu Yanzu: Kotu ta tabbatar da Sanata Adeleke a matsayin dan takarar gwamna na PDP a Osun

Yanzu Yanzu: Kotu ta tabbatar da Sanata Adeleke a matsayin dan takarar gwamna na PDP a Osun

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Osogbo ta tabbatar da Sanata Ademola Adeleke a matsayin sahihin dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Osun
  • Mai shari'a Nathaniel Emmanuel, ya kuma yi watsi da karar da Prince Dotun Babayemi ya shigar na neman a bayyana shi a matsayin dan takarar jam'iyyar adawar a zaben
  • Rahotanni sun nuna cewa za a dai gudanar da zaben gwamnan na jihar Osun ne a ranar 16 ga watan Yulin 2022

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Osun - Alkalin babbar kotun tarayya da ke zama a Osogbo, Justis Nathaniel Emmanuel, ya tabbatar da Sanata Ademola Adeleke a matsayin dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamnan Osun da za a yi a ranar 16 ga watan Yulin 2022, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki

Alkalin ya yi watsi da karar da Prince Dotun Babayemi ya shigar, inda yake neman a ayyana shi a matsayin dan takarar babbar jam’iyyar adawa ta kasar.

Yanzu Yanzu: Kotu ta tabbatar da Sanata Adeleke a matsayin dan takarar gwamna na PDP a Osun
Yanzu Yanzu: Kotu ta tabbatar da Sanata Adeleke a matsayin dan takarar gwamna na PDP a Osun Hoto: bbc.com
Asali: Facebook

Ya kuma soke zaben fidda gwanin da ya samar da Babayemi, wanda aka gudanar a cibiyar taro ta WOCDIF, Osogbo a ranar 8 ga watan Maris, 2022.

Har wayau, Justis Emmanuel ya ayyana cewa Sanata Ademola Adeleke ne sahihin zababben dan takarar PDP a zaben, rahoton The Nation.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Magudi akayi min a 2019, ni na lashe zabe: Atiku Abubakar

A wani labari na daban, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman kujeran shugaba a 2023 karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya jaddada cewa shi ya kashe zaben shugaban kasa a 2019.

Atiku yace kawai jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi amfani da karfin mulki wajen kwace nasarar daga hannunsa.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara

Ya kara da cewa sam ba zasu taba yarda a sake musu irin wannan a zaben 2023 idan jam'iyyar PDP ta bashi tikiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng