Shugaban kasa a 2023: Ni nafi cancanta na gaji Buhari, in ji Saraki
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bugi kirjin cewa shine ya fi cancanta a cikin dukkanin masu neman kujerar shugaban kasa a 2023
- Saraki ya bayyana cewa shine zai iya kawo sauyin da ake bukata a kasar saboda gogewar da yake da shi a bangaren zartarwa
- Ya kuma jadadda cewa a cikin dukkanin masu neman kujerar Buhari a zabe mai zuwa babu wanda yake da gogayya irin tasa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Osun - Tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a ranar Talata, ya ayyana kansa a matsayin mafi cancanta a cikin wadanda ke neman takarar shugaban kasa a 2023.
Saraki ya yi magana ne a Osogbo yayin wata ganawa da shugabanni da mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Osun, jaridar Punch ta rahoto.
Dan takarar shugaban kasar ya kuma bayyana cewa ya kasance kusa da iyalan PDP a jihar, yana mai cewa ya kuma yi aiki tare da su don tabbatar da ganin cewa jam’iyyar adawar ta koma mulki a jihar.
Ya kuma nemi goyon bayan wakilai daga jihar don tabbatar da nasararsa a yayin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce:
“Ni kadai ne dan takarar da ke da gogewa na shekaru takwas a bangaren dokoki, wanda ya kasance a ma’aikata mai zaman kanta, kuma wanda ya kasance shugaban majalisar dokokin tarayya.
“Babu wani mutum da ke da wannan gogewar. Imma kana magana kan kwarewa a bangaren dokoki, ko kana magana game da sauya fasalin lamura wanda suka hada da sake bitar kundin tsarin mulki da gyara ta, kan mutumin da ya jagoranci majalisa, ko kuma kana magana game da hada kan yan Najeriya, ka san cewa majalisar dokokin tarayya wuri ne da za ka fara zuwa a tsakanin sa’anni. Ya zama dole ka kasance da ikon hada kan mutane.
“Za ka fahimci yadda kasuwanci yake don mutane da ke kasuwanci su iya zuba jari. Babu wani dan takara da ke da wannan gogewar kuma wannan ne yasa na yarda cewa ni ne nafi cancanta a tsakaninsu.”
Saraki ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP reshen Osun ta yarda da shi sosai, don haka suka kuduri aniyar kasancewa tare da shi a zaben fidda gwani na shugaban kasa da ke tafe, rahoton Vanguard.
2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara
A wani labarin, rahoton da ya fito daga Daily Trust a ranar Laraba, 18 ga watan Mayu 2022, ya nuna cewa ana rigima tsakanin BOT, NWC da gwamnoni a PDP.
Majalisar NWC ita ce ke rike da jam’iyya, alhakin gudanar da harkokin jam’iyya na yau da kulum ya rataya ne a kan wuyan ‘yan majalisar aiwatarwar.
Ita kuma BOT ce majalisar amintattu wanda ta kunshi dattawan da kan tsoma baki idan ta kama.
Asali: Legit.ng