Jam’iyyar APC ta jero sharudan da za su sa a hana mutum takara a 2023 bayan ya saye fam

Jam’iyyar APC ta jero sharudan da za su sa a hana mutum takara a 2023 bayan ya saye fam

  • Jam’iyyar APC mai mulki ta fitar da tsare-tsaren da za ta bi a wajen fito da masu neman yin takara
  • Sulaiman Argungu ya rantsar da kwamitocin da za su tantance wadanda suke harin tikiti a 2023
  • Argungu ya ce dole a duba takardun biyan kudin fam, da kuma shaidar karatun bokon masu takara

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta na cigaba da shirye-shiryen yadda za ta gudanar da zaben fitar da gwani a karshen watan nan a fadin Najeriya.

Jaridar The Cable ta rahoto Sulaiman Argungu yana bayanin abubuwan za su iya yin sanadiyyar da mai neman kujera zai rasa shiga takara a jam'iyya.

Sulaiman Argungu wanda shi ne sakataren gudanarwa na jam’iyyar, ya bayyana haka ne a wajen rantsar da kwamitin tantance masu neman takara.

Kara karanta wannan

2023: Saura kwana 10 zabe, an shiga yamutsi a PDP game da wanda za a tsaida takara

A ranar Talatar nan aka kaddamar da kwamitocin da za su tantance masu neman kujerar majalisar dokoki da masu kada kuri’u a zaben fitar da gwani.

Za a bi dokar zaben Najeriya

Argungu ya bukaci ‘yan kwamitin su yi aiki da sashe da 84 (3) na dokar zabe na kasa na shekarar 2022 wajen tantance masu takara a zabe mai zuwa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sakataren gudanarwar ya jaddada cewa bai halatta APC ta saba doka wajen tsaida ‘dan takara ba.

Jam’iyyar APC
Shugabannin APC a wajen taro Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Aikin da kwamiti zai yi - APC

A cewar Argungu, aikin kwamitocin sun hada da duba shaidar karatun ‘dan takara da kuma binciken wadanda suka tsaya masa wajen neman mulki.

Har ila yau za a nemi ganin takardun shaidar biyan kudin sayen fam din sha’awa da na takara. Da zarar ba a samu wannan takarda ba, ba za a shiga takara ba.

Kara karanta wannan

Sakamakon umarnin da aka bada, mai ba Buhari shawara ya ajiye aiki domin neman Gwamna

“Sai da takardar biyan kudi na risiti sannan mai neman takara zai iya shiga zabe. Kuma dole a duba su wanene su ke tallafa masu.”
“Idan wani ya sabawa sashe na 84 (3) na dokar zabe wanda aka yi wa kwaskwarima a 2023, to za a cire shi daga cikin ‘yan takaran.”

An rahoto APC tana cewa daga nan za a fitar da sunayen wadanda aka tantance, a mika su a sakatariyar APC domin ba su takardar shiga zaben tsaida gwani.

Jack-Rich zai tsaya takara

An ji labari Tein TS Jack-Rich ya na neman shugaban kasa, ya ce a kowace karamar hukuma zai kirkiri sana’ar da mutane 26, 000 za su yi idan ya karbi mulki.

Idan an yi nasarar yin haka, mutane 20,124,000 za su zama sun kama sana’a daga ranar da TS Jack-Rich ya dare kan kujerar shugaban Najeriya a Aso Rock.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal ya tona ‘Dan Arewan da APC ta ke shirin ta tsaida takarar Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng