Na Shirya Zama Mai Shara a Villa Idan Lawan Ya Zama Shugaban Ƙasa, In Ji Orji Kalu

Na Shirya Zama Mai Shara a Villa Idan Lawan Ya Zama Shugaban Ƙasa, In Ji Orji Kalu

  • Sanata Orji Uzor Kalu, bulaliyar majalisar dattawa ya ce a shirye ya ke ya zama mai shara a fadar shugaban kasa idan Ahmad Lawan ya zama shugaban kasa
  • Tsohon gwamnan na jihar Abia ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jadada goyon bayansa ga takarar shugabancin kasa na Lawan a shekarar 2023
  • Kalu ya ce ba dole sai an bashi wani mukami ba kawai yana goyon bayan Lawan ne saboda cancantarsa da jajircewarsa kuma shugaba irinsa ake bukata a Najeriya yanzu

Sanata Orji Uzor Kalu ya sake jadada goyon bayansa ga takarar shugabancin kasa na Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, yana mai cewa a shirye ya ke ya zama 'mai shara' a Villa idan burinsa ya cika.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Bulaliyar na Majalisa ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin hira da shi da aka yi a shirin Politics Today na Channels Television.

Na Shirya Zama Mai Shara a Villa Idan Lawan Ya Zama Shugaban Ƙasa, In Ji Orji Kalu
Orji Kalu: Na Shirya Zama Mai Shara a Villa Idan Lawan Ya Zama Shugaban Ƙasa. Hoto: Kalu Orji.
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Idan Ahmed Lawan ya zama shugaban kasa, a shirye na ke in zama mai shara a wurin (Aso Rock). Ba sai an bani mukami ba idan Ahmed Lawan ya zama shugaban kasa," in ji tsohon gwamnan na Jihar Abia.
"Zan iya sharar Villa; gida na kusa ya ke da Villa. Zan iya zama mai sharar Villa; babu nisa tsakanin mu. Ba ba'a na ke yi ba."

A cewar tsohon gwamnan, takarar ta Lawan na samun nasara ta yadda wasu yan takarar ke janye wa shugaban majalisar na dattawa.

"Ina fada maka, na yi magana da yan takarar shugaban kasa guda tara, kuma sun ce a shirye suke su janye wa Ahmed Lawan," dan majalisar ya kara cewa.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Kalu, wanda ya ce Najeriya na bukatar jajirtaccen shugaba, ya yi imanin Lawan ne zai iya bawa kasar wannan shugabancin.

"Na san shi tsawon shekaru 41 da suka shude," sanatan ya ce. "Dakin mu daya a jami'a. Jajirtacce ne, zai iya bawa Najeriya shugabancin da ake bukata."

Ya kara da cewa an samu nasarori sosai a bangaren yin dokoki a majalisar karkashin jagorancin Ahmed yana mai cewa zai maimaita hakan a kasa idan an zabe shi shugaban kasa.

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

Kara karanta wannan

Dan Marigayi Abiola Ya Shiga Jerin Masu Son Gaje Kujerar Buhari, Ya Siya Fom Din Takara

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel