Matashi ‘Dan shekara 38 ya fito zai jarraba sa'a a takarar Shugaban kasa a zaben 2023

Matashi ‘Dan shekara 38 ya fito zai jarraba sa'a a takarar Shugaban kasa a zaben 2023

  • Onyeka Nwafor ya shaidawa Duniya cewa zai yi takara a jam’iyyar National Rescue Movement
  • A ranar Asabar Onyeka Nwafor ya ayyana shirin neman shugaban Najeriya a wajen wani taro a Awka
  • Matashin ya zargi shugabanni da rashin kula da matasa, ya bayyana gwamnatinsa za ta banbambta

Anambra - Jaridar nan ta Telegraph ta fitar da rahoto a karshen makon da ya gabata wanda ya nuna cewa Onyeka Nwafor zai yi takarar shugaban kasa.

Onyeka Nwafor mai shekara 38 da haihuwa zai nemi kujerar shugaban Najeriya a zabe mai zuwa da za ayi a 2023 a karkashin jam’iyyar hamayya ta NRM.

Dr. Onyeka Nwafor likita ne wanda ya shiga siyasa, ya kuma zabi jam’iyyar National Rescue Movement domin cin ma burinsa na shugabancin kasa.

Kamar yadda rahotanni suka zo mana jiya, Nwafor ya ayyana niyyar yin takara a wani otel mai suna Golden Mars Hotel da ke garin Udoka, a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

Shugabanni sun kyale matasa - Nwafor

Da yake jawabi a garin Awka, jaridar Punch ta rahoto matashin yana mai zargin tsofaffin shugabanni da aka yi da watsi da matasa a cikin lissafinsu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nwafor yana ganin wadanda suka yi mulki a kasar nan sun gagara cin moriyar sa’o’insa a Najeriya.

Takarar Shugaban kasa a zabe
Taron siyasa a Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: UGC
“A shekarun da aka yi, zababbu da sauran shugabannin da aka nada a gwamnati sun sa tulin matasanmu masu ilmi da ake da su, duk sun cire rai.”

Abubuwa sun lalace a Najeriya

“Sun cire rai da kasar nan saboda rashin maida hankali wajen cika alkawuran da suka dauka lokacin yakin neman zabe ko manufar jam’iyyarsu.”
“Tasirin wannan ya bayyana karara wajen tabarbarewar tattalin arzikinmu, lalacewar harkar ilmi, sukurkucewar tsaro, da sake a sha’anin banki.”

- Onyeka Nwafor

Nwafor ya ce sauran matsalolin kasar a yau sun hada da rugujewar kasuwanci, matsalar tsarin karbar haraji, rashin ayyukan yi, da rikicin kabilanci da addini.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Buhari fa na da dan takarar da yake so ya gaje shi, Adesina ya magantu

Idan har Nwafor ya kafa gwamnati a 2023, ya yi alkawarin gyara harkokin ilmi, kiwon lafiya, tsaro da rashin wutar lantarki domin kawo karshen matsalar kasar.

A daina raina NNPP

A zaben 2023, NNPP za ta ba mutane mamaki a filin zabe. Dazu aka rahoto Farfesa Rufai Ahmed Alkali yana cewa a rubuta wannan zancen da ya yi, a kuma ajiye.

Rufai Ahmed Alkali ya ce idan suka kafa gwamnati, za a inganta tsaro, a habaka tattalin arziki, a samu ayyukan yi ta hanyar dawo da masana'antun da suka lalace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng