Ministar Buhari ta lashe amanta, ta janye daga takarar kujerar sanata
- Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta hakura ta janye daga tseren kujerar sanata mai wakiltan yankin Filato ta kudu a babban zaben 2023
- Tallen ta bayyana cewa ita da kanta ta janye daga tseren kujerar bayan ta tuntubi iyalai da yan uwanta
- Ta kuma ce ta yanke hukuncin ne domin ta tabbatar da manufofin gwamnatin Shugaba Buhari na ciyar da mata gaba
Abuja - Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta janye daga kudirinta na takarar kujerar sanata a babban zaben 2023 mai zuwa.
Tallen wacce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu, ta kuma ce bata yi murabus daga matsayinta na minista ba, Daily Trust ta rahoto.
Ta bayyana cewa ta yanke hukuncin ne domin ta samu damar mayar da hankali kan tubalin da aka gina wajen ci gaba da tabbatar da daidaiton jinsi a mukaman shugabancin kasar nan.
A ruwayar The Cable, Tallen ta ce ita da kanta ta janye daga tseren bayan ta tuntubi iyalai da yan uwanta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ce:
“Tare da godiya mai tarin yawa da tawali’u, na yanke shawarar janyewa daga takarar Sanata wanda na shiga saboda kira-kiraye daga mata da sauran ’yan Najeriya masu kishin kasa wadanda suke ganin akwai bukatar a samu babbar muryar da za ta wakilci mata a majalisar dattawa bayan sun tattauna da iyalina, 'yan uwa da magoya bayana kan rawar da nake takawa mata a Najeriya a yau.
“Saboda haka, ga dukkan matan Najeriya da kananan yara mata wadanda suka nuna damuwa kan abun da zai biyo baya, ina basu tabbacin cewa ni, Dame Pauline K. Tallen, OFR, KSG ban mika takardar ajiye aiki ba.
“Kuma saboda haka, hukuncin karan kaina ne cewa ba zan ci gaba da wannan bukatar ba amma zan ci gaba a matsayin ministar harkokin mata.”
A cewarta, jajircewar shugaba Buhari na ciyar da mata gaba ya sa ta ga akwai bukatar ta ci gaba a matsayin minista, wanda hakan zai taimaka wajen magance matsalolin da suka shafi mata da yara.
“Kasarmu na da dadadden alkawari na shawo kan kalubalen da ke hana mata kawo sauye-sauye masu kyau da kuma abubuwan da ake bukata idan aka ba su damar yanke shawara.
“Nada ni a matsayin ministar harkokin mata alama ce ta wannan ci gaba kuma ba zan iya mantawa da wannan damar ba."
A ranar 8 ga watan Mayu ne Tallen ta sanar da cewa za ta shiga takarar kujerar sanata mai wakiltan yankin Filato ta kudu a babban zaben 2023.
Tsohon ministan Buhari ya magantu kan rade-radin janyewa daga tseren shugaban kasa
A wani labarin, tsohon ministan harkokin Neje Delta, Sanata Godwill Akpabio, ya ce bai janye daga tseren takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba.
A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, a ranar Lahadi, Akpabio ya ce jita-jitan da ke yawo na cewa ya hakura da takarar kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari abun dariya ne.
Tsohon ministan ya jadadda cewa yana nan daram-dam a cikin tseren, yana mai cewa zai lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki.
Asali: Legit.ng