Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari ya fadi ranar da zai yi murabus, zai dukufa ga takara

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari ya fadi ranar da zai yi murabus, zai dukufa ga takara

Ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya yi nuni da cewa zai yi murabus a ranar Litinin mai zuwa bisa bin umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba mambobin majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) da ke neman tsayawa takara.

Ministan ya bayyana hakan ne a Kaduna a ranar Lahadi a lokacin da ya ziyarci jihar domin duba goyon bayan da wakilan jam’iyyar APC za bashi a zaben fidda gwani na shugaban kasa.

Ya nuna godiya ga Buhari bisa damar da ya samu na zama minista a mulkinsa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Amaechi ya jaddada harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna da cewa, ba zai faru ba idan da majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kwangilarsa ido da ya bukata a layukan dogo.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel