Bayan ziyarar Ganduje, Shekarau ya fasa sanar da komawarsa jam'iyyar NNPP

Bayan ziyarar Ganduje, Shekarau ya fasa sanar da komawarsa jam'iyyar NNPP

  • Sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya ta gaza yanke shawara kan zama a APC ko komawa NNPP
  • Shekarai, wanda tsohon gwamnan Kano ne ya yanke shawarar komawa NNPP amma sai ya samu ziyara daga wajen Ganduje
  • Amma wasu na kusa da shi na cewa bai fasa ba, ranar Litinin Shekarau zai sauya shekarsa

Kano - Sanata Ibrahim Shekarau, dan majalisa mai wakiltan Kano ta tsakiya a majalisar dattijai ya dakatad da shirin sauya sheka daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa New Nigeria Peoples Party (NNPP).

Amma mai magana da yawunsa, Sule Ya'u Sule, ya bayyanawa manema labarai yau Asabar cewa an dakatad da sauya shekan zuwa ranar Litinin, rahoton Vanguard.

A cewarsa, an dakatar da sauyar daga "yau Asabar amma za'ayi ranar Litinin."

Kara karanta wannan

Labari ya canza bayan Ganduje ya hakura da neman takarar ‘Dan Majalisar Dattawa a 2023

Sule Ya'u bai bayyana dalilin dage taron sauya shekan ba amma ana kyautata zaton bai rasa alaka da ziyarar da gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ya kai gidan Shekarau daren Juma'a.

Shekarau
Bayan ziyarar Ganduje, Shekarau ya fasa sanar da komawarsa jam'iyyar NNPP
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dirakta Janar na sabbin kafafen yada labaran Shekarau, Isnaila Lamido, ya sanar da cewa an dakatar da taron sauyan shekan.

A cewarsa:

"An shirya yin taron ranar Asabar a gidan Ibrahim Shekarau amma an dakatar, za'a sanar da sabon rana nan ba da dadewa."
"Akwai wasu tsare-tsare masu muhimmanci da ya kamata a kammala da dattawan jihar wanda ya hada Rabiu Kwankwaso da Ibrahim Shekarau kafin a sanar da sabon rana."

Kwankwasiyya ta samu karuwa, shugaban yakin neman zaben Tinubu ya rungumi NNPP

Abdulmumin Jibrin wanda yana cikin manyan masu yi wa Bola Tinubu yakin zama shugaban Najeriya, ya shiga jam’iyyar hamayya ta NNPP.

Kara karanta wannan

Rikicin siyasar Kano: A yau Shekarau zai fice daga APC, zai hade da Kwankwaso

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa tsohon ‘dan majalisar na yankin Kiru/Bebeji ya sauya-sheka zuwa jam’iyyar NNPP a ranar Juma’a, 13 ga watan Mayu, 2022.

Hon. Abdulmumin Jibrin yana cikin wadanda aka gani a filin sauka da tashin jirgin saman Malam Aminu Kano wajen tarbar Sanata Rabiu Kwankwaso.

Tsohon Gwamnan na Kano ya dawo daga birnin tarayya Abuja tare da wasu manyan ‘yan siyasa da suka sauya-sheka kwanan nan daga APC zuwa NNPP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel