‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023
- Mista Tein Jack-Rich ya shiga takara, ya na harin kujerar Muhammadu Buhari da zai sauka a 2023
- Attajirin ya nada tsohon gwamna Isa Yuguda ya zama shugaban yakin neman zabensa a jam’iyyar APC
- Da yake jawabi, Jack-Rich ya sha alwashin habaka tattalin arzikin Najeriya ba tare da cin bashi ba
A ranar Juma’a, 13 ga watan Mayu 2022, aka samu labarin cewa Tein Jack-Rich yana da niyyar tsayawa takarar shugaban Najeriya a zaben 2023.
Jaridar Punch ta ce Tein Jack-Rich yana so ya nemi kujerar shugaban kasa ne a jam’iyyar APC.
Tuni dai har Mista Tein Jack-Rich ya saye fam din neman zama ‘dan takarar shugaban Najeriya a APC a kan kudi N100m, har ya kuma cike fam dinsa.
Inda za a san da gaske Rich yake yi, ya nada tsohon gwamnan jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda a matsayin shugaban kwamitin yakin neman zabensa.
‘Yan shekara 40 masu takara
Zuwa yanzu Jack-Rich yana cikin masu kananan shekaru da suke harin kujerar shugaban kasa. Mafi yawan masu takara a APC ‘yan 60 ne zuwa 70.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Baya ga Rich mai shekara 47, akwai Nicholas Felix ‘dan shekara 48 da ke neman takara, sai kuma Gwamna Yahaya Bello da zai cika shekara 47 a bana.
Marayan da ya zama Attajiri
Da yake yi wa magoya bayansa jawabi a garin Abuja, ‘dan siyasar ya bada labari mai ratsa jiki na yadda ya taso a matsayin maraya a garin Fatakawal.
Sannu a hankali Rich ya kafa kamfanin Belemaoil Producing Limited wanda ya zama ‘dan gida na farko a yankin Neja-Delta da yake hako danyen mai.
Mai neman takarar ya karanta ilmin harkar mai a makarantar Panola College Cartage ta Amuka, ya kuma samu ilmin kasuwanci a wata jami’a a Wales.
Zan gyara tattalin Najeriya
Kamar yadda The Cable ta kawo rahoto, Jack Rich ya yi alkawari ba zai ci bashi ba idan ya zama shugaban Najeriya, ya ce zai habaka tattalin arzikin kasa.
Roch ya ce birnin Kalifoniya na kasar Amurka bai wuce girman Legas da Ogun ba, amma karfin tattalin arzikinsu ya kai $3.6tr, yayin da Najeriya ke fama.
Jonathan zai shiga takara
Bisa dukkan alamu tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan zai yi takara a zaben 2023. A ranar Juma'a ne mu ka kawo maku wannan rahoto.
A jiya aka yi tunanin kungiyar da ta sayawa tsohon shugaban kasar fam za ta maida fam din da aka cike. Hakan zai nuna Jonathan zai nemi mulki a 2023.
Asali: Legit.ng