Igbo bai da amana, bamu yarda a ba su shugabancin kasa ba: Kungiyoyin Arewa CNG

Igbo bai da amana, bamu yarda a ba su shugabancin kasa ba: Kungiyoyin Arewa CNG

  • Wasu kungiyoyin Arewa sun bayyana rashin amincewarsu da baiwa dan kabilar Igbo shugabancin kasa a Igbo
  • A cewar gamayyar kungiyoyin, yan siyasar kabilar Igbo basu da amana saboda kalaman da suka yi kwanan nan
  • Kungiyoyin sun yi watsi da kalaman dattawan Igbo inda suke kira ga lallai mulki ya koma yankinsu

FCT, Abuja - Gamayyar kungiyoyin Arewa CNG a ranar Alhamis, 12 ga Mayu, sun yi watsi da kalaman da kungiyoyin Igbo ke yi na cewa wajibi ne a baiwa Igbo mulkin Najeriya a 2023.

Kakakin kungiyar CNG, AbdulAzeez Suleiman, a hirarsa da manema labarai da wakilin Legit.ng ya halarta, ya ce Igbo basu da amana kuma basu mulki na da hadari.

Ya kara da cewa dattawan Igbo na kokarin tada tarzoma bisa gargadin da suka yi kwanan cewa zasu tada rigima a kasar nan idan ba'a baiwa yankinsu mulkin zama shugaban kasa bayan shugaba Muhammadu Buhari ba.

Kara karanta wannan

2023: Matasan CAN Sun Bayyana Abin Da Za Su Yi Wa Duk Ɗan Takarar Da Bai Fito Fili Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Ɗalibar Da Ta Zagi Annabi Ba

Kungoyoyin Arewa CNG
Igbo bai da amana, bamu yarda a ba su shugabancin kasa: Kungoyoyin Arewa CNG Hoto: CNG
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya caccaki dattawan Arewan bisa kiran da suka yiwa shugaba Buhari na ya saki shugaban kungiyar IPOB na ya saki Nnamdi Kanu.

"Dattawan Igbo kuma dai sun sake kokarin tada tarzoma ranar 4 ga Mayu, 2022 inda suka ce idan ba'a baiwa yankinsu shugabancin kasa a 2023 ba, kasar za ta iya rikidewa cikin rikici da bala'i."
"CNG ta lura da cewa wadanda ke wadannan kalamai marasa amfanin na son tayar da rikici a kasa saboda a sake wani yaki basasa kuma ya kashe mutane."
"Hakan na zurfafa tsoron da muke na ganin kada a sake a baiwa Igbo shugabancin kasa kuma wadannan kalamai sun tabbatar da haka."

Ka saki Nnamdi Kanu: Shugabannin Igbo sun kalli Buhari ido da ido, sun roki alfarma

Shugabannin yankin Kudu maso Gabas sun bukaci da a gaggauta sakin shugaban tsagerun IPOB, Nnamdi Kanu daga tsare shi da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi.

Kara karanta wannan

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

Shugabannin sun yi wannan roko ne a wata tattaunawa da suka yi da Buhari a zauren majalisar zartarwa da ke gidan gwamnati a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Buhari ya kai ziyarar aiki ta kwanaki biyu a jihar Ebonyi, kamar yadda rahotanni daga fadar shugaban kasa da gwamnatin Ebonyi ta bayyana, The Nation ta ruwaito.

Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya na Kudu maso Gabas, Eze Charles Mkpuma ne ya karanta jawabin nema wa Kanu afuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng