Yanzun Nan: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Yanzun Nan: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

  • Mr Olawepo-Hashim, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya sanar da janye takararsa a yau Juma'a
  • Hashim ya ce wasu dalilai ne suka taso don haka ya dakatar da batun takarar amma hakan baya nufin zai dena gwagwarmaya don cigaban Najeriya
  • Hashim ya yi godiya ga magoya bayansa, wadanda suka taya shi da addu'a da wadanda suka karfafa masa gwiwa yana mai cewa lokacinsa na zuwa a gaba

Abuja - Bayan tuntuba da shawarwari kan halin da siyasa ke ciki a yanzu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Mr Gbenga Olawepo-Hashim ya janye takararsa a zaben 2023, ya ce 'ranarsa za ta zo', rahoton Leadership.

A sanarwar ofishin watsa labaransa ta Abuja ta fitar a ranar Juma'a, Mr Olawepo-Hashim ya ce duk da cewa ya shiga APC ne domin yin takara da nufin kawo sabuwar Najeriya, wasu 'abubuwa sun taso da suka tilasta masa janye wa daga takarar shugaban kasar ta 2023' don haka bai siya fom ba.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu

Yanzun Nan: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa
'Dan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa. Hoto: The Nation.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa hakan ba ya nufin ya karaya daga anniyarsa na samar da sabuwar Najeriya, inda ya samu magoya baya da dama, amma wani lokacin abin da ake bukata sun fi niyya, shiri da jajircewa.

Ya kuma ce bai yi watsi da mafarkin cewa wata rana zai zama shugaban kasa ba kamar yadda ya ke ciki sakonsa da Premium Times ita ma ta rahoto.

"Amma a yanzu dole in janye saboda abin da ya fi zama alheri ga kasa, ba ni ne abin da ya fi muhimmanci ba, kasa ce," in ji shi.

Ya mika godiyarsa ga wadanda suka nuna masa goyon baya da addu'a yana mai tabbatar musu cewa janye takarar baya nufin ya dena gwagwarmayarsa na ganin an samu nagartacciyar Najeriya.

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

A wani rahoton, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164