Sabon salo: Birkitaccen mawaki ya fito takarar gaje Buhari a jam'iyyun siyasa har biyu
- Mawakin da ke yawan jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, Portable shi ne a baya-bayan nan ya fito fili ya bayyana cewa zai tsaya takarar shugabancin Najeriya
- Mawakin ya bayyana haka a shafinsa na Instagram inda ya bayyana cewa zai tsaya takarar kujera ta daya a dandalin jam’iyyun siyasa biyu mabambanta
- Ya wallafa hoton yakin neman zabensa a Instagram sannan ya yada hade da takaitaccen bayanin manufarsa, ‘yan Najeriya sun mayar da martani kan labarin nasa
Najeriya - Shahararren mawakin Najeriya, Portable ya sa jama'a a shafukan sada zumunta suna ta maganganu bayan da ya yada hoton yakin neman zabensa a Instagram.
Mawakin ya bayyana sha'awarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa amma a jam'iyyar APC da SDP duk dai a lokaci guda.
A taken kamfen din nasa, ya bayyana cewa lokaci ya yi da jama'ar tituna za su mamaye gwamnati yayin da ya bayyana a manufarsa.
A cewarsa:
"Yan uwana 'yan Najeriya naji kukanku kuma na yanke shawarar tsayawa takarar shugaban kasa a tarayyar Najeriya, mu sa Najeriya ta sake tafiya. Zeh."
Ga sakon da ya wallafa a kasa:
Jama'ar kafar sada zumunta a fadin kasar sun mayar da martani daban-daban game da sanarwar da Portable ya yi na tsayawa takarar shugabancin kasa, inda akasarinsu ke mamakin yadda ya samu shiga cikin jam'iyyun siyasa biyu.
Legit.ng ta dauko wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a kamar haka:
Deejayneptune:
"Mutumin da ke da jam'iyyu biyu wanne za mu zaba a ranar zabe?"
Alama_200:
"Kai kadai ke dauke jam'iyyun siyasa biyu a fosta daya."
Oung_big_sky:
"Shugaban Wahala."
King_sinzu_chase:
"Idan kayi takara dan uwa zan tafi saboda kai naje nayi PVC."
Tuateba:
"Shugaban titi, zan zabe ka."
Goodluck Jonathan ba zaiyi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba
A wani labarin, alamu sun nuna cewa da yuwuwar tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Jonathan, ba zai nemi takarar shugaban kasa ƙarƙashin APC ba.
Vanguard ta gano cewa Fom din APC na miliyan N100m da kungiyar Fulani ta saya wa Jonathan a makon nan, har yau ba'a cike shi ba bare a maida wa jam'iyya.
A yau Jumu'a, 13 ga watan Mayu, 2022 jam'iyyar APC ta tsara rufe karɓan Fom daga hannun yan takara bayan sun kammala cike wa.
Asali: Legit.ng