Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

  • Bisa dukkan alamu tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan zai yi takara a zaben 2023
  • Goodluck Ebele Jonathan zai jarraba sa’arsa a zaben shugaban kasa wannan karo a jam’iyyar APC
  • A yau ake tunanin kungiyar da ta sayawa tsohon shugaban kasar fam za ta maida fam din da aka cike

FCT Abuja - Tsohon shugaban kasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya saduda, zai shiga neman takarar shugaban Najeriya da za ayi a shekara mai zuwa.

A wani rahoto da Punch ta fitar a ranar Juma’a, 13 ga watan Mayu 2022, ta tabbatar da cewa maganar yin takarar Goodluck Ebele Jonathan ta kankama.

Ana zargin wasu masu ruwa da tsarki a jam’iyyar APC mai mulki sun kammala shirye-shiryen yadda za a tsaida Jonathan a matsayin ‘dan takara a 2023.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

Wata kungiyar Arewa da ta ikirarin ‘ya ‘yanta Fulani ne ta fitar da Naira miliyan 100, ta fanshi fam din shiga takarar shugaban kasa da sunan Dr. Jonathan.

Wannan mataki da kungiyar ta dauka ba tare da tuntubar tsohon shugaban Najeriyan ba ta fusata shi, hakan ta sa da farko ya ki karbar fam din na su.

Amma daga baya an shawo kan Mai girma Jonathan, ya amince ya jarraba sa’arsa a zabe mai zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jonathan
Jonathan da Buhari Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A cewar wannan kungiya, a yau Juma’a ne za ta maidawa uwar jam’iyyar APC fam din da aka cike da sunan fitaccen ‘dan siyasar domin ya sake neman mulki.

Legit.ng Hausa za ta saurari yadda za a gabatar da wannan fam an jima. Ana sa ran sakataren shirye-shirye na APC, Sulaiman Argungu ne zai karbi fam din.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Goodluck Jonathan ba zai yi takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ba

Kowa ya maida fam dinsa

Idan hakan ta tabbata, Jonathan zai zama kusan na karshe da ya maida fam din neman tutar APC.

A karshen makon nan ne aka ji cewa Yahaya Bello da Bola Tinubu sun maida fam dinsu. Wadannan biyu su na cikin wadanda suka fara ayyana takara.

Mun samu labari cewa ‘ya ‘yan jam’iyya sama da 400 suka rattaba hannu a kan fam din Tinubu. Hakan ya nuna yadda ya karbu a cikin masu tsaida ‘dan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng