2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari

2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari

  • Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya samu goyon bayan takwaransa na jihar Gombe, Inuwa Yahaya a kokarinsa na son gaje Shugaba Buhari
  • Yahaya ya bayyana cewa tarin sanin da Fayemi ke da shi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya sa ya cancanci darewa kujerar
  • Gwamnan na Gombe ya bayyana tarin ilimi, kuzari da kwarewar Fayemi daga cikin abubuwan da za su sanya shi yin abun kirki idan ya zama shugaban kasa

Gombe - Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya bayyana cewa gwamnan jihar Ekiti kuma mai son zama shugaban kasa, Kayode Fayemi, na da tarin ilimi da iyawar da kasar ke bukata a wannan mawuyacin yanayi.

Femi Ige, kakakin tawagar kamfen din Kayode Fayemi, ne ya nakalto gwamnan na Gombe yana fadin haka a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu, jaridar The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Fayemi ya ziyarci takwaran nasa a Gombe a ranar Laraba.

2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari
2023: Gwamna Inuwa Yahaya ya lamuncewa Kayode Fayemi don ya gaji shugaba Buhari Hoto: @kfayemi
Asali: Twitter

Yahaya ya ce gwamnan na Ekiti ya rike mukaman shugabanci daban-daban kuma hakan ya sanya shi zama mafi cancanta a cikin yan takarar shugaban kasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce:

“Fayemi na da tarin kwarewa, kuzari, da ilimi mai zurfi.
“Wadannan sune abubuwan da Najeriya ke bukata a wannan mawuyacin yanayi. Dan uwana Fayemi, kana da cikakken goyon bayanmu saboda mun yarda cewa Najeriya na bukatarka.
“Na yarda da iyawarka kuma ina karfafa maka gwiwar fitowa domin wannan babban aiki kuma ina farin ciki da ganin cewa ka shiga tseren.”

A bangarensa, Fayemi ya ce idan aka zabe shi zai bayar da fifiko kan tsaro, tattalin arziki da samar da aikin yi, rahoton Vanguard.

Duk mu na goyon bayan Bola Tinubu a zaben Shugaban kasa – El-Rufai ya dauki matsaya

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

A wani labarin, mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fito karara, ya shaidawa Duniya cewa yana goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Jaridar Daily Trust ta ce Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne a lokacin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ‘yan gayyarsa suka kai ziyara zuwa Kaduna.

Jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya ziyarci garin Kaduna a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu 2022 domin samun goyon baya a zaben fitar da gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng