Duk mu na goyon bayan Bola Tinubu a zaben Shugaban kasa – El-Rufai ya dauki matsaya
- A yau ne Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya karbi Bola Tinubu da ‘yan tawagarsa
- Gwamnan ya tabbatarwa Duniya cewa ‘ya ‘yan APC na Kaduna duk su na tare da takarar Bola Tinubu
- Nasir El-Rufai ya gyara kalaman Kashim Shettima da ya ce El-Rufai zai marawa Tinubu baya a zaben APC
Kaduna - Mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fito karara, ya shaidawa Duniya cewa yana goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Daily Trust ta ce Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne a lokacin da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da ‘yan gayyarsa suka kai ziyara zuwa Kaduna.
Jagoran na jam’iyyar APC mai mulki ya ziyarci garin Kaduna a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu 2022 domin samun goyon baya a zaben fitar da gwani.
Wadanda suka yi wa Tinubu rakiya sun hada da na hannun damansa, Kashim Shettima da kuma tsohon shugaban hukumar EFCC na kasa, Nuhu Ribadu.
Ana tare da El-Rufai - Shettima
Da yake jawabi a wajen ganawar, Sanata Kashim Shettima ya shaidawa ‘yan jam’iyyar APC na reshen jihar cewa Gwamna El-Rufai yana goyon bayansu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da ya tashi zai yi jawabi, Malam El-Rufai ya yi karin haske a kan abin da tsohon gwamnan na jihar Borno ya fada, ya nuna za su marawa tafiyarsu baya.
Wuka da nama bai hannu na - El-Rufai
Mai girma El-Rufai ya tabbatar da cewa ba zai yiwu ya goyi bayan takarar Tinubu ba, har sai idan sauran ‘ya ‘yan jam’iyyar APC sun yi na’am da mai takarar.
“Ina so in gyara abin da Kashim Shettima ya fada, da ya ce Gwamna yana tare da su (Tinubu).”
“Kafin in tabbatar da abin da Shetima ya fada a nan, ina so in tabbatar daga wajen masu zaben ‘yan takarar mu. Shin ku na tare da Asiwaju.”
- Nasir El-Rufai
Rahoton ya ce wadanda suke halartar taron jam’iyyar ta APC suka amsa a tare da cewa ‘Eh!”
“Ran ka ya dade, ina yin duk abin da suka fada mani ne, su ne iyayen gida na. Haka jam’iyyar APC ta ke aiki a jihar Kaduna.” – Nasir El-Rufai.
Yakin zaben fitar da gwani
Legit.ng ta samu labari cewa Bola Ahmed Tinubu ya tsaya a Kaduna ne a zagayen da yake yi na neman goyon-bayan ‘ya ‘yan APC bayan ya baro jihar Gombe.
A makon nan aka ji labari, jam’iyyar PDP ta bakin Debo Ologunagba ta ce ana biyan N100m ana sayen fam a APC ne saboda a tara kudin yin kamfe da wayau.
Abin da doka ta ce shi ne bai halatta a kashe sama da N5bn wajen yakin neman zaben shugaban kasa ba. Kawo yanzu, APC ta tara biliyoyi daga kudin saida fam.
Asali: Legit.ng