2023: Ministan Buhari ya bayyana abun da zai yi kafin ya bi umurninsa na yin murabus
- Ministan kwadago da daukar ma’aikata, Chris Ngige, ya yi martani ga umurnin shugaban kasa da ya bukaci yan majalisarsa da ke neman takara a 2023 su yi murabus
- Ngige ya ce kafin ya sauka daga kujerarsa, zai tuntubi shugaban kasa Buhari da al’ummar mazabarsa
- Ministan wanda ke son ya gaji Buhari a 2023 ya kuma bayyana cewa shugaban kasar ya bayar da damar da za a tuntube shi
Abuja - Ministan kwadago da daukar ma’aikata, Dr Chris Ngige, ya bayyana cewa zai tuntubi shugaban kasa Muhammadu Buhari da al'ummar mazabarsa kafin ya yi murabus daga matsayinsa a majalisar zartarwa ta kasar.
Ministan na martani ne ga umurnin da shugaban kasa Buhari ya bayar a ranar Laraba, 11 ga watan Mayu, cewa dukka mambobin majalisarsa da ke hararar kujerun siyasa a 2023, su yi murabus kafin ranar 16 ga watan Mayun 2022, Leadership ta rahoto.
Ngige, wanda ya yi magana bayan taron majalisar zartarwa a Abuja a ranar Laraba, ya kara da cewar shugaban kasar ya bayar da wata kafa da duk wanda ke neman karin bayani a kan furucinsa zai tuntube shi.
Vanguard ta nakalto Ngige na cewa:
“Ban da martani a yanzu saboda shugaban kasar ya ce idan wani na son karin bayani, toh ya same shi.
Don haka ya zama dole na tuntube shi sannan na tuntubi mazabata, jihar Anambra saboda ina rike da mukamin ne don gwamnati da mazabata.”
Buhari Ya Umurci Su Amaechi, Malami, Ngige Da Akpabio Su Yi Murabus Cikin Kwana 5
A baya mun ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya umurci dukkan ministocinsa da ke son yin takara a zaben 2023 da ke tafe su mika takardan murabus dinsu kafin ko ranar Litinin 16 ga watan Mayun 2022, Channels Television ta rahoto.
Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan yayin da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Villa a Abuja.
Daga cikin ministocin da suka ayyana niyyarsu na takara akwai Rotimi Amaechi (Sufuri), Chris Ngige (Kwadago), Abubakar Malami (Shari'a), Godswill Akpabio (Neja Delta).
Asali: Legit.ng