2023: Tsohon Sanata Hayatu Gwarzo, ya zama mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewa maso Yamma
- Tsohon sanata mai wakiltan Kano ta arewa, Bello Hayatu Gwarzo, ya zama mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na arewa maso yamma
- Attah Aidoko Alli, shugaban kwamitin zaben ne ya sanar da hakan a ranar Talata, 10 ga watan Mayu
- Gwarzo ya samu kuri'u 426 wajen kayar da abokin hamayyarsa Mohammed Yusuf, wanda ya samu kuri’u 313
Kano - An zabi tsohon sanata mai wakiltan Kano ta arewa, Bello Hayatu Gwarzo, a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na arewa maso yamma.
Attah Aidoko Alli, shugaban kwamitin zaben ne ya sanar da sakamakon zaben a daren ranar Talata, jaridar The Cable ta rahoto.
Ya ce Gwarzo ya samu kuri’u 426 wajen lallasa abokin hamayyarsa Mohammed Yusuf, wanda ya samu kuri’u 313.
Alli ya ce an zabi sauran mukamai da suka hada da na sakatare, ma’aji, sakataren shiri da shugabar mata ta hanyar maslaha, jaridar Daily Post ta rahoto.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An dage taron bayan yan bindiga sun tarwatsa shirin wanda aka yi a watan Afrilun 2021 a Kano.
Taron na PDP ya kaure da rikici bayan magoya bayan Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan Kano, sun kara da masu yiwa Aminu Tambuwal na jihar Sokoto biyayya.
A lokacin, tsagin H. A. Tsanyawa, Sakataren PDP a Kano, ya zargi Kwankwaso da jagorantar ‘yan daba wajen hargitsa taron.
Zaben 2023: PDP ta fallasa 'dabarar' da ta sa Jam’iyyar APC ta saida fam a kan N100m
A wani labarin, jam’iyyar hamayya ta PDP ta zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da jagorantar ‘wawurar dukiyar al’umma’ domin a tunkari zabe mai zuwa.
Daily Trust ta bayyana cewa Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba ya zargi gwamnatin APC da tara kudin sata da sunan fam din takara.
A jawabin da ya fitar a ranar Talata, 10 ga watan Mayu 2022, Debo Ologunagba ya ce jam’iyyar hamayyar ta ga bukatar ankarar da mutane halin da ake ciki.
Asali: Legit.ng