Shirin 2023: Tinubu ya samu 'delegate' 370, ya mika fom dinsa na takarar gaje Buhari
- Labarin da ke iso mu yanzun nan ya bayyana cewa, dan takarar shugaban kasa Bola Tinubu ya cike fom dinsa ya mika wa APC
- Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da jam'iyyar ta sanar da rufe sayar da fom din gabanin zaben fidda gwani
- Rahoto ya nuna cewa, wasu jiga-jigan APC ne suka taru domin mayar da fom din na Tinubu da tsakar ranar Labara 11 ga watan Mayu
Jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya mayar da cikakken fom dinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyarsu ta APC a yau dinnan.
Tinubu ya mika fom din ga ofishin jam’iyyar ne a ranar Laraba 11 ga watan Mayu a dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal; tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Nuhu Ribadu, da dai sauransu ne suka wakilci Tinubu.
Jaridar Punch ta tattaro cewa, Tinubu ya samu wakilan jam'iyya 370 daga sassan kasar nan daban-daban domin kammala mika fom dinsa na takarar shugaban kasa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A baya dai an ruwaito cewa a matsayin sharadi na mika fom din tsayawa takara, jam’iyya mai mulki ta umarci ‘yan takararta na shugaban kasa su mika fom din dauke da sa hannun wakilai 10 daga kowace jiha da kuma babban birnin tarayya.
Wakilin Punch ya ce ya ga fom din, ya kuma lura cewa, ana bukatar kowane dan takara ya samu sa hannun wakilai 370 da suka kunshi jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya.
Wakilin Legit.ng Hausa ya bi shafin sada zumunta na masu yakin neman zaben Tinubu, ya gano hotunan jiga-jigan APC da suka dawo da fom din na Tinubu.
Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takarar kujerar Sanata
A wani labarin na daban, gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi Fom din takarar kujerar Sanata na jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Dan siyasan mai shekaru 72 a duniya na shirin wakiltar mazabar Kano ta Arewa a majalisar dattawan tarayya.
Ganduje, zai kara da Sanata Barau Jibrin wanda ke rike da kujeran tsawon shekaru bakwai yanzu. Ganduje ya rike matsayin mataimakin gwamna karkashin Rabiu Kwankwaso 1999-2003 sannan suka sake tafiya tare 2011-2015.
Asali: Legit.ng