Dan takarar shugaban kasa mai shekaru 35 ya kai karar PDP kan kudin fom N40m
- Har ila yau, an yi ta caccakar yadda jam'iyyun siyasa suka fita da tsadar kudin fom din takarar shugaban kasa a wannan karon; zaben 2023
- A wannan karon jam’iyyar adawa ta PDP za ta fuskanci shari’a domin wasu ‘ya’yanta da ba su ji dadin tsadar fom ba sun fusata
- Masana harkokin siyasa da basu ji dadin tsadar ba sun bayyana cewa wani yunkuri ne hakan na korar ‘ya’yan jam’iyyar masu karamin karfi
Wani dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Mista Ayoola Falola, a ranar Talata ya garzaya wata babbar kotun tarayya da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, yana neman soke tsarin zaben fidda gwani na jam’iyyar gabanin 2023 mai zuwa zabe.
Karar da ya shigar tana kalubalantar jam’iyyar ne kan kudin fom har N40m domin nuna sha’awa da tsayawa takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Falola ya gama hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da kuma shugaban jam’iyyar na kasa Iyorchia Ayu a cikin karar da ya shigar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito..
A karar, Falola ya ce jam’iyyar ba ta da hurumin kakaba ka’idojin neman biyan fom din tsayawa takara da kuma nuna sha’awarsu daga 'yan takara ko kuma duk wani mamba da ke da muradin tsayawa takarar kujerar gwamnati a jam’iyyar gabanin babban zabe mai zuwa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Da yake ambaton sashe na 84 (3) na dokar zabe ta 2022 da sashe na 65, 66,106, 107, 131, 137, 177, 187, 224, 224 da 15(2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya 1999, wanda ya shigar da karar ya nemi kotu ta rusa kudurin jam'iyyar tasu.
Ya kuma bayyana cewa INEC na da ikon sa ido a kan ayyukan PDP; kakabawa a kundin tsarin mulkin jam'iyyar, ka’idojinta da kuma karin sharuddan tantance sunayen ‘yan takara ko rashin cancantarsu.
Ba wannan ne karon farko da PDP za ta samu irin wannan kara ba, wani dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar, Okey Uzoho shi ya shigar da irin wannan, kamar yadda Pulse ta ruwaito.
Yau ake yin ta a PDP, za a dauki mataki a kan wadanda za a ba tikitin Shugaban kasa
A wani labarin, idan ba a samu wata matsala ba, a yau Laraba, 11 ga watan Mayu 2022, jam’iyyar hamayya ta PDP za ta yi zaman babbar majalisar koli watau NEC. Jaridar Daily Trust tace za ayi wannan taro da aka dade ana jira ne hedikwatar PDP da ke Abuja.
Batutuwan da za a tattauna a kan su a wajen wannan taro sun kunshi rahoton kwamitin mutum 37 da ya yi aiki a kan yankin da ya dace a mikawa takara.
Zaman NEC din da za ayi yau shi ne zai zama na 97 tun da aka kafa PDP a 1998. A taron za a amince da wurin da za a shirya zaben tsaida ‘dan takara.
Asali: Legit.ng