Gwamnan Legas ya cika baki a kan tazarce ganin an gagara samun mai takara da shi a APC

Gwamnan Legas ya cika baki a kan tazarce ganin an gagara samun mai takara da shi a APC

  • Babajide Sanwo-Olu ya cike fam din neman takarar Gwamnan Legas a karkashin jam’iyyar APC
  • Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa yana sa ran sake samun nasara a zabe mai zuwa
  • Bisa dukkan alamu jam’iyyar APC ba za ta bata lokaci wajen zaben tsaida ‘dan takara a Legas ba

Abuja - Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya maida fam din da ya saya na sake neman takarar kujerar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar APC.

Premium Times ta ce a ranar Talata, 10 ga watan Mayu 2022, Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya maida fam din da ya cike a babban dakin taro na ICC a Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya, Babajide Sanwo-Olu ya nuna cewa ya na mai sa ran za a sake zaben shi saboda ayyukansa da aka gani a shekaru uku.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

Gwamnan ya fadawa ‘yan jarida cewa gwamnatinsa ta yi nasarar canza halin da Legas ke ciki, duk da annobar COVID-19 da aka yi fama da ita na dogon lokaci.

“Mun bunkasa garin nan a kan yadda aka san shi a shekaru uku zuwa hudu kafin mu karbi mulki. Yanzu ya fi kowane samun kudi daga waje saboda an samu tsaro.”
Gwamnan Legas
Bola Tinubu ya daga hannunsu Babajide Sanwo-Olu Hoto: jidesanwooluofficial
Asali: Facebook

Babu mai neman tikiti a APC?

Legit.ng Hausa ta fahimci babu wani wanda ya yanki fam din neman Gwamna a Legas bayan Sanwo-Olu. Hakan na nufin kai-tsaye gwamnan zai samu tuta.

A tarihin jihar Legas kuwa, PDP ba ta taba karbe mulki ba tun da aka dawo tsarin farar hula a 1999. Sanwo-Olu ne gwamna na hudu da aka yi a shekara 20.

Kara karanta wannan

Jonathan ya amsa kiran masoyansa, yau za a gabatar da fam din shiga takararsa a APC

Idan za a tuna, shekaru hudu da suka wuce Akinwumi Ambode ya rasa samun tikitin jam’iyyar APC duk da yana kan kujerar gwamna, hakan ta sa bai zarce ba.

Kamar yadda TVC ta kawo rahoto, wani gwamna mai neman tazarce da babu wanda ya yi tarayya da shi wajen sayen fam shi ne Babagana Umara Zulum.

Taron ‘Yan siyasan Yarbawa a kan 2023

Vanguard ta ce Sanwo-Olu ya yi magana a kan zaman da aka yi da masu neman shugaban kasa a jam’iyyar APC daga yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Sanwo-Olu ya ke cewa Bisi Akande da Segun Osoba su ka kira wannan taro da kusan kowa ya samu halarta, amma ba a iya samun abin da ake so a zaman ba.

Osinbajo ya karbu a Gombe

An ji cewa Yemi Osinbajo ya kai ziyara domin gaida Mai martaba Sarkin Gombe, Abubakar Shehu Abubakar a fadarsa bayan ya hadu da 'ya 'yan jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Ciwon zuciya zai kama wasu: Gwamnan CBN ya ce burinsa na gaje Buhari na bashi dariya

Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya nuna goyon bayansa ga takarar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo yake son yi a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng